Na Hannun Dama Ya Ba Tinubu Shawara Ya Jawo Kwankwaso da Peter Obi a Gwamnati
- Dr. Kayode John Fayemi yana cikin wadanda suka yi gaggawan taya Bola Tinubu murnar lashe zabe
- Tsohon Gwamnan jihar Ekiti ya yi alwashin gwamnatin APC ba za ta ba ‘Yan kasa kunya a mulki ba
- Fayemi ya bada shawarar a tafi tare da abokan karawan 2023, da alama Tinubu zai rungumo ‘yan adawa
Abuja - Tsohon Gwamnan Ekiti ya fitar da jawabin taya murna ga ‘dan takaran APC. The Cable ta ce Kayode John Fayemi ya yabi tsohon mai gidansa.
Dr. Kayode John Fayemi ya ce sanin kan siyasa, basira da dabara suka taimakawa Tinubu ya lashe zabe, ya kuma ce zai dage wajen kawo siyasar cigaba.
Daga bayanin da ya yi, an ji tsohon Ministan tarayyar yana yin kira ga shugaban kasa mai jiran-gado da ya kafa gwamnati tare da abokan hamayya.
“Ina taya Shugaban kasa mai jiran-gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar nasararsa a zaben shugabancin Najeriya na 2023.
An fafata a zaben da ya yi sanadiyyar yi wa Asiwaju sakayyan kokari da manufarsa ga Najeriya.
Idan dai Asiwaju da na sani ne, gwamnatinsa za tayi kokari wajen inganta rayuwar talaka, ta kawo zaman lafiya, hadin-kai da inganta tattali.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ko da cewa Asiwaju ‘dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC ne, zai kasance shugaban ‘Yan Najeriya, ya kawo adalci da daidaito.
APC ba za ta bada kunya ba
A jawabin da Fayemi ya fitar a ranar Laraba, ya mika sakon godiya ga ‘yan kwamitin PCC, ‘yan jam’iyya da duk wadanda suka bada gudumuwarsu.
Fayemi wanda yayi Gwamna sau biyu a Ekiti ya ce ba za su ba mutanen kasa kunya ba, ya ce gwamnatin Tinubu za ta cika alkawuran da ta dauka.
Ina so in yi kira ga wanda ya yi nasara da jam’iyyarmu da su yi tunann kafa gwamnatin hadin kai ganin irin kokarin da jam’iyyun hamayya suka yi.
A wannan zabe mai tarihi, babu wanda ya yi galaba, kuma babu wanda aka yi galaba a kan shi, yanzu lokaci ne na murnar jajircewar ‘yan kasa.
Maganar da Tinubu ya yi dazu
A bangarensa, an ji wanda ya yi nasara, yana godewa magoya bayan sauran jam'iyyu da suka kada kuri’arsu, ya ce yanzu lokacin siyasa ya wuce.
Tsohon gwamnan na Legas ya ce duk da Atiku, Obi da Kwankwaso abokan adawarsa ne, 'yanuwansa ne, ya yi kira gare su da su zo a hada-kai tare.
Buhari ya yi wa Bola Tinubu barka
Kamar yadda labari ya zo da safiyar nan, Shugaban Najeriya ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben sabon shugaban kasa da aka yi a makon jiya.
Malam Garba Shehu ne ya fitar da jawabi a madadin Muhammadu Buhari bayan nasarar APC, ya ce Tinubu ya fi kowa cancanta a jerin masu takaran.
Asali: Legit.ng