Buhari Ya Yi Maganar Nasarar Tinubu da APC, Ya Gargadi Atiku, Obi da Kwankwaso
- Shugaban Najeriya ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben sabon shugaban kasa da aka yi
- Malam Garba Shehu ne ya fitar da jawabi a madadin Muhammadu Buhari bayan nasarar APC
- Shugaba Buhari ya ce a jerin wadanda suka fito neman kujerarsa, Tinubu ya fi kowa cancanta
Abuja - An tabbatar da wanda ya lashe zaben sabon shugaban kasa a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ne zai karbi mulki a hannun Muhammadu Buhari.
Malam Garba Shehu wanda yake magana da yawun shugaban kasa, ya fitar da jawabi, yana mai kira ga wadanda suka sha kayi a zaben da su tafi kotu.
The Cable ta rahoto Garba Shehu yana cewa zanga-zanga ba zai haifar da komai ba sai tashin-tashina.
Mai girma shugaban kasa ya yi alkawarin za a gyara harkar zabe, ganin cewa jama’a sun yi korafi a game da gazawar INEC na daura sakamako a yanar gizo.
"Tinubu ya fi dacewa da mulki"
Da yake taya Bola Tinubu murna, shugaba Muhammadu Buhari ya ce ‘dan takaran ne ya fi kowa cancanta a wadanda suka nemi kujerarsa a zaben da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabinsa, Buhari ya ce a shirye yake da ya ga ya mikawa sabon shugaban Najeriya mulki.
Abin da Buhari ya fada
Ina taya Mai girma Bola Ahmed Tinubu murnar nasararsa. Mutane su ka zabe shi, shi ne ya fi dacewa da wannan kujera.
Zan yi aiki da shi da mutanensa wajen ganin an mika mulki yadda ya kamata.
Wannan zabe shi ne mafi girman sha’anin damukaradiyya a Afrika. Yankin da yake fama da juyin-mulki a shekarun bayan nan.
An ja kunne a kan zanga-zanga
Duk yadda abokan gaba za su ji babu dadi wajen karbar sakamakon, idan sun ji bukatar kalubalantar zaben, sai su garzaya gaban kotu, ba kan titi ba.
Idan su ka hau titi, ya nuna ba kishin al’umma ne a gabansu ba, sai dai neman jawo rikici, us jefa al’umma a hadari saboda son kai da abin da za su samu."
- Muhammadu Buhari
Zaben Sanatocin 2023
Ku na da labari jam’iyyar APC mai mulki ta na da duka Sanatocin jihohin Legas, Ogun, Ekiti, Ondo, Kwara, Oyo, Kogi, Katsina da Ebonyi.
Jam’iyyar adawa ta PDP kuwa ta samu duka kujerun da ke mazabun Osun da jihar Kaduna. LP ta samu Sanatoci a Kudu maso gabas da Abuja.
Asali: Legit.ng