Shugaban Kasa: Jam’iyyar Labour Party Ta Lashe Zabe a Jihar Cross River
- Peter Obi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya yi kasa-kasa da abokan hamayyarsa a jihar Cross River
- Obi ya lallasa Atiku Abubakar na PDP da Bola Tinubu na APC a zaben na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu
- APC ta lashe kujerun yan majalisa biyar, PDP ta samu biyu yayin da Labour Party ta tashi da daya
Cross River - Dan takarar jam'iyyar Labour Party(LP), Peter Obi, ya lashen zaben ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu da aka yi a jihar Cross River, rahoton Premium Times.
Obi ya samu kuri'u 179,917 wajen lallasa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu wanda ya samu kuri'u 130,520.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na uku da kuri'u 95,425, rahoton The Nation.
A majalisar dokokin tarayya a jihar, Labour Party ta samu kujera daya kacal daga cikin kujeru takwas na mazabun tarayya a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A sauran kujeru bakwai da suka rage, jam'iyyar APC ta lashe guda biyar yayin da PDP ta tashi da guda biyu.
A kujerun sanatoci uku da aka yi, APC ta lashe biyu yayin da PDP ta ja guda daya.
Ga rabe-raben sakamakon zaben a kasa:
Jimlar masu zabe da aka yi wa rijista 1691642
Jimilar masu zabe da aka tantance 444880
Jimilar ingantattun kuri'u 416968
Lalatattun kuri'u 24608
Jimilar kuri'u da aka kada 441576
Kuri'u da manyan jam'iyyun siyasa hudu da suka samu
APC 130520
Labour Party: 179917 - Ita ta lashe zabe
NNPP 1644
PDP 95425
Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Delta
A wani lamari makamancin wannan, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya lallasa manyan abokan hamayarsa a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu da aka yi a jihar Delta.
Baturen zaben INEC a jihar, Farfesa Owunari Abraham Georgewill, ne ya sanar da haka a Asaba, babban birnin jihar.
Obi ya lashe zaben da kuri'u da yawansu ya kai 341,866, yayin da mai bi masa, Atiku na PDP ya samu kuri'u 161,600.
Asali: Legit.ng