Peter Obi Ya Lallasa PDP a Jihar Abokin Takarar Atiku Abubakar

Peter Obi Ya Lallasa PDP a Jihar Abokin Takarar Atiku Abubakar

  • Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP kuma gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya gaza kawo wa Atiku jiharsa
  • A sakamakon zaben da INEC ta sanar tun a matakin jihar, Peter Obi ne ke kan gaba da kuri'u mafi rinjaye
  • Zaben bana ya zo abubuwan ban mamaki ta yadda manyan jiga-jigan siyasa suka gaza tabbatar da nasarar jam'iyyarsu a jihar da suka fito

Delta - Mista Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, ya tumurmusa abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da zaɓen ranar Asabar a jihar Delta.

Daily Trust tace Baturen zaben INEC mai alhalin tattara sakamako a jihar, Farfesa Owunari Abraham Georgewill, ne ya sanar da haka a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Atiku Abubakar da Peter Obi.
Atiku ya sha ƙasa a hannun Peter Obi Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar ya nuna Peter Obi ne ya samu nasara da ƙuri'u 341,866, yayin da mai biye masa, Atiku na PDP ya samu kuri'u 161,600.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa: Peter Obi Ya Lallasa Atiku Da Tinubu a Jihar Cross River

Legit.ng Hausa ta gano cewa sakamakon ya nuna Mista Obi ya baiwa Atiku tazarar kuri'u 180,266.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Delta mai ci, Ifeanyi Okowa, shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 vanguard ta rahoto.

Yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ya kasance a jihar Delta

ADC - 160

ADP - 788

APC - 90,183

APGA - 3,746

APM - 1,028

APP - 493

BP - 1,016

LP - 341,866

NNPP - 3,122

MRM - 988

PDP - 161,600

PRP - 334

SDP - 3,071

YPP - 605

ZLP - 3,324

Adadin kuri'un da aka kaɗa - 615,342

Adadin kuri'un da suka lalace - 39,309

Zakamakon Zabe: Atiku Ya Samu Nasara a Sakkwato da Kebbi

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasarar lashe kuri'u mafi yawa a jihohin arewa guda biyu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Obi Atiku? INEC Ta Fadi Wanda Ya Lashe Zabe a Kogi

A sakamakon zaben shugaban kasa da ya fito daga bakin baturen zaɓe na jihar Kebbi, Atiku ne ya lashe jihar da kuri'u masu yawa, Bola Tinuɓu na take masa baya.

Haka zalika a jihar Sakkwato, tsohon mataimakin shugaban kasan ya sha da kyar a hannun takwaransa na jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel