Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Kasa-Kasa Da Atiku Da Obi a Jihar Kogi

Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Kasa-Kasa Da Atiku Da Obi a Jihar Kogi

  • Hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Kogi
  • Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe zabe a jihar Kogi da yawan kuri'u 240,751
  • Tinubu ya lallasa sauran manyan abokan hamayyarsa da suka hada da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP

Kogi - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta ayyana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar a jihar Kogi.

Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu tsaye
Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Kasa-Kasa Da Atiku Da Obi a Jihar Kogi Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Adadin kuri'un da kowani dan takara ya samu

Baturen zaben INEC, Farfesa Wahab Egbenwole, ya ayyana a ranar Talata cewa Tinubu ya samu kuri'u 240,751 wajen lallasa babban abokin adawarsa, Atiku Abubakar na PDP wanda ya samu 145,104.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku Abubakar Ya Ɗaga Sama, Ya Samu Nasara a Ƙarin Jihohin Arewa 2

Har ila yau, ya ce dan takarar Labour Party, Mista Peter Obi, ne ya zo na uku da kuri'u 56,217, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewar daga cikin masu zabe 484,884 da aka tantance don zabe a jihar, 476,038 ne suka kada kuri'u, kuma cewa kuri'u 456,790 ne aka samu a matsayin masu inganci yayin da aka yi watsi da 19,248.

Tinubu ya lashe kananan hukumomi 15 da suka hada da: Mopa/Muro, Kogi, Kabba Bunu, Ijumu, Igala/ Mela da Yagba West, Olamaboro, Ofu ,Yagba East, Dekina, Ankpa, Lokoja, Okene and dah da Ajaokuta.

A daya bangaren, Atiku ya lashe kananan hukumomi shida da suka hada da: Ogori Magogo, Adavi, Bassa, Ibaji, Okehi da Omala.

INEC ta ayyana zaben Zamfara ta tsakiya a matsayin ba kamalalle ba

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: INEC Ta Sanar da Sakamakon Jihar Zamfara, Atiku da Kwankwaso Sun Sha Kashi

A wani labarin, hukumar zabe ta INEC ta ayyana zaben majalisar dokokin tarayya na Zamfara ta tsakiya a matsayin ba kamalalle ba bayan soke wasu rumfunar zabe.

Hakazalika INEC ta ayyana zaben dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar tarayya na Gusau/Tsafe da aka yi a ranar Asabar a matsayin ba kamalalle ba.

Kamar yadda turawan zaben na majalisun dokokin tarayya a yankin suka sanar, hukumar zaben za ta sanar da sabon rana da za a sake zabe don cike guraben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel