Yadda aka Kirkiro Dabarar Hana Malamin Musulunci Kada Kuri'a a Zaben Shugaban Kasa

Yadda aka Kirkiro Dabarar Hana Malamin Musulunci Kada Kuri'a a Zaben Shugaban Kasa

  • Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya ce da gan-gan aka rika ki kawo kayan aiki a wasu filayen zabe
  • Shehin malamin na Islama ya koka cewa an zo da dabarun ne domin hana Bayin Allah yin zabe a Sokoto
  • Farfesa Mansur Sokoto yana ganin Shugaban kasa ya wahalar da kan shi ne a wajen hana sayen kuri’u

Sokoto - Babban malamin addinin musuluncin nan, Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya kokagame da yadda aka hana su kada kuri’a a zaben shugaban kasa.

A wani rubutu da ya yi a dandalin Facebook a ranar da aka yi zabe, Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya ce an kawo dabara domin tauye masu hakki.

Malamin hadisin ya ce jami’an INEC ba su zo rumfarsu da kayan aiki ba sai karfe 3:00 na rana, bayan makararar, sai kuma aka nuna masu babu takardun kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

Sheikh Mansur Sokoto ya ce ya bada shawarar ayi amfani da takardun da aka zo da su domin wadanda suke kan layi su samu damar yin zabe tukuna a rumfar.

Inda aka fara samun matsala

Wakilan jam’iyyun siyasar da aka turo ba su yarda da shawarar malamin ba, hakan ta sa aka tuntubi ma’aikatan hukumar INEC domin su iya kawo isassun takardu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da jin irin abin da yake faruwa, malamin a rumfar ya bada labari cewa sai hukumar zabe ta ce sam ba za ta yiwu a kada kuri’a alhali karfe 4:30 na maraice ta wuce ba.

Duk da cewa tun bayan sallar asuba mutane suka fito wurin zabe, sai aka roki malaman INEC suyi hakuri jama’a su kada kuri’arsu ga ‘yan takaran da suke kauna.

Wannan alfarama ba ta samu shiga ba, daga nan Shehin ya ce suka gano an kirkiro dabarar ne tun farko domin a hana wasu yin zabe a inda ba a hangen nasara.

Kara karanta wannan

Karin bayani: INEC ta dage zaben shugaban kasa a rumfuna 141 na wata jiha

Malam zabe
Wani yana kada kuri'a a zabe Hoto: institute.global
Asali: UGC

"An hana ni zabe!"

“Wata kisisina ce da aka kulla a wasu rumfuna masu yawa a nan Sokoto cikin su har da rumfar da nake jefa kuri'a.
Tun da farko an ce mana injimin tantance jama'a ne ba a ba ma'aikatan ba. An kawo shi karfe 3:30nr sai kuma suka ce, babu isassun ballot papers.
Karfe 5:30ny muka ce a fada mana guda nawa ke akwai, suka ce 102, na ba da shawarar ayi hakuri mutane su shiga layi ayi ma wadanda suke nan saboda a lokacin ba mu kai wannan adadin ba, sai agents din wata jam'iyya suka ce ba su yarda ba.
Na yi communicating da jami'ai aka ce an san da wannan matsala kuma ga su nan za a kawo, sai suka ce ai su ba za su yarda ayi zabe ba tun da 4:30 ta wuce kuma shi ne lokacin da aka shata za a kare zabe.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Ta'adda Sun Kai Kazamin Hari Kan Masu Kaɗa Kuri'a a Borno

Duba da cewa tun karfe 6ns wasu suke wurin, jama'a sun roki agents din alfarma su bari ayi, suka ce ai su nasu jama'ar tuni sun tafiyar su don haka lallai ba za su bari ayi zabe ba.
Daga nan ne na samu labarin cewa strategy ne aka yi don hana zabe a wasu rumfuna daga wasu wadanda ke ganin ba za su samu rinjaye a wajen ba.
Lallai kam a Najeriya muna ganin dimukradiyya. Allah ya kyauta.
Mansur Sokoto
25 Febrairu 2023”

Baba Buhari bai fahimci Najeriya ba.

Har ila yau da ya ke magana a shafinsa, babban malamin ya ce binciken da ya yi a matsayinsa na wakilan AANI a wajen aikin zabe, ya nuna masa abin mamaki.

Mansur Sokoto ya ce an yi amfani da jami’an tsaro zuwa wasu rumfuna domin su watsa borkonon tsohuwa saboda a fatattakin mutanen da suka fito yin zabe.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Abba Kyari Ya San Matsayarsa a Kotu, Alkali Ya ce Zai Yi Zabe a Kurkuku

Farfesan ya ce da kyar ya tsira daga jifan da jama’a suke yi wa jami’an tsaron da ke wannan aiki.

Kudi sun yi aiki a zaben 2023

A gefe guda, malamin addinin ya ce ya ga yadda aka rika rabon sababbin kudi, buhunan shinkafa, atamfofi da wayoyin zamani domin a saye kuri’un talakawa.

“Na ce, ko ya ya aka yi yan siyasa suka samu wadannan kudin masu wuya wadanda Baba Buhari ya killace su ya ce kada a fito da su sai an gama zabe?
Iyawa da dan Najeriya sai Allah! Da Baba Buhari ya san haka da bai sa mu a cikin wannan kunci da takura saboda matsalar da bai iya magancewa ba.
Allah ya kyauta.

LP ta bada mamaki

Ku na da labari manyan Jam’iyyun siyasa na APC da PDP sun sha kasa a rumfunar zaben fadar Aso Villa a hannun Peter Obi da ya tsaya takara a LP.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Ambaci Matsala 1 da Za a Iya Fuskanta a Gobe

A wuraren da ake tunanin APC za ta samu gagarumar nasara a Legas, Peter Obi ya samu kuri’un da har suka zarce na Bola Tinubu da ya tsayawa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng