Duk da Jam’iyyar APC Tana da Gwamna, Atiku Ya Koyawa Tinubu Hankali a Jihar Arewa
- Babu wani gari da da Bola Tinubu da APC suka iya yin galaba a kan Atiku Abubakar a jihar Gombe
- ‘Dan takaran na PDP ya lallasa jam’iyyar APC mai-mulki a duka kananan hukumomin da ke Gombe
- PDP ta samu kuri’u fiye da 300, 000 a Balanga, Yamaltu/Deba, Nafada, Kaltungo, Gombe da dai sauransu
Gombe - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta lashe duka kananan hukumomin da ake da su a jihar Gombe a zaben shugaban Najeriya da aka gudanar.
Rahoton Daily Trust na safiyar Litinin ya tabbatar da cewa Atiku Abubakar mai takara a PDP ya yi galaba a kan Bola Tinubu a jihar Gombe.
Yayin da ‘dan takaran na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 319,123, Bola Ahmed Tinubu ya samu 146,977 ne daga kananan hukumomi 11 da ke jihar.
Shugabar jami’ar tarayya da ke Gashua, Farfesa Maimuna Waziri ta sanar da sakamakon zaben.
Yadda sakamakon zaben ya kasance
Kamar yadda Farfesa Waziri ta bayyana, Atiku ya samu 13,520 a Shongom, APC kuma ta tashi da 7,525, LP da NNPP sun samu 7,525 da kuma 256.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Atiku yana da kuri’u 23,326 a Balanga shi kuma Tinubu ya samu 11,715, Obi yana da 3,760 yayin da ‘dan takaran NNPP, Kwankwaso ya samu 405.
A Nafada, PDP ta samu kuri’u 12,339, inda APC ta tashi da 8,242, NNPP ta samu 344, LP tana da 7. Jaridar Leadership ta kawo wannan rahoto dazu.
Kuri’u 25,384 Atiku Abubakar ya samu a karamar hukumar Funakaye, APC kuwa ta samu 12, 672. NNPP da LP sun tsira ne da 767 da kuma 320.
Kuri’un Yamaltu/Deba sun nuna PDP ta na 38,479, sai APC ta samu 18,896. A nan NNPP ta samu 1,591 sannan kuri’u 740 su ka je ga Peter Obi na LP.
A Kwami LGA, PDP ta ci 24,068, APC ta samu 16,245, NNPP 820, LP 78. PDP ta samu 21, 991 a Billiri, LP ta ci 8, 898 sai Bola Tinubu ya samu 7, 232.
Kuri’u 21, 579 PDP ta samu a Dukku, yayin da APC ta kare da 12,925, sai NNPP 899. Rahoton ya ce haka abin yake a Akko, Kaltungo da garin Gombe.
An ki karbar kuri’u 16, 000 na PDP
Malamin zaben hukumar INEC na jihar Delta, Farfesa Abraham Georgewill Owuneri ya ki karbar sakamakon zaben kauyensu Dr. Ifeanyi Okowa.
Ku na da labari INEC ta ce mutum 30, 105 aka tantance a Ika ta Arewa maso gabas, amma kuma mutum 31, 681 suka yi zabe a kauyen Gwamnan.
Asali: Legit.ng