An Sanar Da Wanda Ya Lashe Zabe A Akwatin Gwamna Tambuwal

An Sanar Da Wanda Ya Lashe Zabe A Akwatin Gwamna Tambuwal

  • Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi nasarar lashe akwatin zabensa da ke Government Girls Secondary School a garin Tambuwal
  • Tun kafin gudanar da zaben, shugaban na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku-Okowa ya riga ya ce duk yadda sakamako ta fito zai rungumi kaddara
  • Amma yayin da sakamakon zabukan suka fita, sun nuna cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ce ta lashe dukkan zabukan shugaban kasa, sanata da na majalisar jiha a akwatin na Tambuwal

Jihar Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya kawo akwatinsa mai lamba 003 da ke makarantar Government Girls Day Secondary School, Tambuwal.

Tambuwal, wanda shine direkta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku-Okowa, ya na takarar kujerar majalisar dattawa ta Sokoto South a zaben.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Yan Siyasa 6 Da Suka Gaza Kawowa Dan Takarar Da Suke Goyon Baya Rumfar Zabensu

Gwamna Tambuwal
Gwamna Tambuwal sanye da babban riga da hula mai ruwan bula. Hoto: Pulse Nigeria
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto cewa sakamakon da aka samu ya nuna cewa dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, ya samu kuri'u 250 yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu ya samu kuri'u 44.

Sakamakon zaben sanata ya nuna PDP ta samu kuri'u 252, ita kuma APC ta tashi da kuri'u 45. Sai na karshe a zaben yan majalisun wakilai na tarayya, PDP ta samu kuri'u 247, sannan APC ta samu kuri'u 48.

Tambuwal: Zan amince da duk sakamakon da ya fito

Tunda farko, gwamnan na Sokoto, Tambuwal ya ce jam'iyyarsa za ta amince da duk sakamakon da ya fito a zaben ta dangana da Allah.

Tambuwal ya bayyana hakan ne lokacin da ya yi jawabi a garinsu da ke karamar hukumar Tambuwal a jiya (Asabar) kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu Ya Lallasa Atiku da Kwankwaso, Ya Lashe Zabe a Kananan Hukumomi 10

Ya ce jam'iyyar PDP ta yarda da bin doka da oda.

Kalamansa:

"Mun yi imani cewa dukkan abin da ya samu dan adam daga Allah ne kuma Allah ne ke bada mulki ga wanda ya so."

Peter Obi ya kayar da Bola Tinubu a akwatin zaben shugaban kamfen dinsa

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Simon Lalong ya kasa kawo wa mai gidansa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuri'u mafi rinjaye a akwatinsa.

Gwamna Lalong shine shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023.

Peter Obi na jam'iyyar Labour shine ya lashe kuri'u mafi yawa a akwatin zaben Lalong.

Asali: Legit.ng

Online view pixel