Atiku ya Samu Tulin Kuri’u a Delta, Hukumar INEC ta ki Amincewa da su, ta Kawo Hujja
- Jami’in da ke tattara zaben jihar Delta bai gamsu da sakamakon zaben Ika ta Arewa maso gabas ba
- Abraham Georgewill Owuneri ya nuna adadin wadanda suka yi zabe sun ce wadanda aka tantance
- A karshe Farfesan bai karbi sakamakon zaben yankin da abokin takarar Atiku Abubakar ya fito ba
Delta - Hukumar zabe na kasa da ke aiki a jihar Delta, ta ki amincewa da wasu sakamakon zabe da aka gabatar mata saboda zargin an yi ba daidai ba.
A wani rahoto da Punch ta fitar a ranar Lahadi, 26 ga watan Fubrairu 2023, an ji cewa INEC ba ta amince da sakamakon da aka kawo daga yankin Ika ba.
‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP kuma Gwamna mai shirin barin-gado, Ifeanyi Okowa ya fito ne daga garin Ika ta Arewa maso gabas.
Rahoton ya ce Hukumar da ke zama a garin Asaba, ta ki karbar sakamakon zabukan da suka fito daga karamar hukumar saboda zargin an yi aringizo.
Da walakin; goro a miya
Jami’an INEC sun ce akwai alamun tambaya a game da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya daga mazabun wannan yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Ifeanyi Okowa yana fata jam’iyyar PDP tayi nasara domin Atiku Abubakar ya lashe zabe.
Malamin da ke tattara kuri’un Delta, Farfesa Abraham Georgewill Owuneri ya ce ba zai karbi sakamakon ba domin masu kada kuri’a sun yi yawa.
This Day ta ce adadin wadanda aka tantance ba su kai yawan mutanen da suka kada kuri’a ba.
Mutum 1, 500 sun karu a rajista
Jami’in zaben da ya yi aiki a karamar hukumar Ika ta Arewa maso gabas, Dr. James Olisa ya ce mutane 30, 105 aka tantance domin su kada kuri’a.
Amma a karshe an samu mutane 31, 681 da suka yi zabe a wannan gari da ke mutane 130, 247 a rajistar INEC, wannan ya jawo abin tambaya a Asaba.
A sakamakon zaben da James Olisa ya gabatar, an fahimci PDP ta na da kuri’u 16, 696, yayin da jam’iyyar LP ta samu 8, 908 sai APC ta tashi da 1, 902.
NNPP: Maraya ya ci zabe a Kano
Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil ya samu kujerar Wudil da Garko a Majalisar Tarayya a Kano a sanadiyyar rasuwar mahaifinsa a makon jiya.
Kamar yadda labari ya zo a yammacin Lahadi, Hon. Kamilu Ado Wudil ya rasu ne a lokacin da ake shirya-shiryen yin zabe, sai yaronsa ya gaje shi.
Asali: Legit.ng