Zaben 2023: Daga Karshe: Primate Ayodele Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa

Zaben 2023: Daga Karshe: Primate Ayodele Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa

  • Kasa da sa'o'i 24 ga babban zaben Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan wanda zai lashe zaben
  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya ce dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zaben
  • A gobe Asabar 25 ga watan Fabrairu ne za a fafata tsakanin Atiku, Bola Tinubu, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ne zai zama shugaban kasa na gaba.

Malamin addinin ya bayyana cewa Allah ya baiwa Atiku Abubakar aikin shugabantar Najeriya na zango daya idan har ya lashe zaben.

Yan takarar shugaban kasa rike da lasifiku
Zaben 2023: Daga Karshe: Primate Ayodele Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

A wata sanarwa daga hadiminsa, Oluwatosin Osho, Ayodele ya lissafo wasu daga cikin ayyukan da suka hada da sauya fasalin kasa, gyara ma'aikatar ilimi, rage farashin man fetur da farfado da tattalin arzikin.

Kara karanta wannan

Zullumi A Sansanin Atiku Da Obi Yayin Da Babban Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Koma Bayan Tinubu

Sai dai kuma, ya gargadi Atiku a kan yin watsi da duk manufofin Allah idan ba haka ba zai gamu da fushin Allah, Nigerian Tribune ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan yan Najeriya basu zabi Atiku ba za su sha wahalar da ta fi ta da - Primate Ayodele

Ayodele wanda ya yi ikirarin cewa ba wai yana yi wa dan takarar na PDP kamfen bane, ya ce idan bai ci zabe ba, yan Najeriya za su sha wahala fiye da wanda suka sha a gwamnatocin baya.

Kalamansa:

"A tsakanin wadannan yan takara uku, Allah ya baiwa Atiku aikin gyara kasar cikin shekaru hudu.
"Idan ya ci zabe sannan ya ki yi wa mutane abun da Allah ke so, zai gamu da fushin Ubangiji.
"Ba zai kammala wa'adinsa ba saboda fushin Allah zai sauka a kansa. Aikinsa shine kafa gwamnati da za ta tafi da kowa, ya kula da tsaro cikin watanni shida, sauya fasalin lamura kafin karshen wa'adin mulkinsa, ya rage farashin man fetur, ya gyara ma'aikatar ilimi, ya farfado da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Zaben bana: Sheikh Dahiru Bauchi ya fadi dan takarar da 'yan Tijjiniya za su zaba ranar Asabar

"Kada ya fara siyar da arzikin Najeriya ga abokansa kuma idan ya aikata haka, zai gamu da fushin Allah. Idan Allah ya taimake shi ya kai wurin sannan ya yi watsi da duk wadannan manufofin, fushin Allah zai sauka a kansa.
"Ba wai ina cewa Atiku zai lashe zabe bane, kuri'un mutane ne zai tabbatar da haka amma kawai ina sanar da abun da Allah ya aike ni na fadawa yan Najeriya ne, Atiku na da aikin da Allah ya daura masa na gyara kasar cikin shekaru hudu.
"Zabi ya rage gareku ku zabe shi ko kada ku zabe shi amma idan bai ci zabe ba, mutumin da ya ci zai kara wa yan Najeriya wahala ne kamar yadda aka rubuta a littafi. Mutanen za su sha wahala fiye da yadda suka sha a gwamnatocin baya."

Kada ka wuce shekaru hudu idan ba haka ba za ka hadu da fushin Allah - Ayodele ga Atiku

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Babban Abinda Ya Sa Atiku Abubakar Zai Iya Rashin Nasara a Zaben Ranar Asabar

Malamin addinin ya bukaci Atiku da kada ya wuce shekaru hudu, yana mai cewa Allah ya zabe shi a matsayin amsar matsalar da Najeriya ke ciki a yanzu kuma cewa idan ya yi wasti da shi, za a fuskanci karin matsaloli, rahoton Daily Post.

Ya kara da cewar:

"Atiku, Ubangiji ya ce na fada maka cewa idan ka ci zabe, lallai kada ka wuce shekaru hudu idan ba haka ba za ka gamu da fushin Allah. Dole ka tafi da kowa a gwamnati, ka sauya fasalin tsaro, lafiya da komai don saita Najeriya. Idan ba ka yi haka ba, Allah zai yi fushi da kai."

A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyun adawa guda 10 sun yi mubaya'a ga takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyart APC a zaben ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng