Magana Ta Fito: Babban Abinda Zai Ja Wa Atiku Faɗuwa Zaben Shugaban Kasa 2023

Magana Ta Fito: Babban Abinda Zai Ja Wa Atiku Faɗuwa Zaben Shugaban Kasa 2023

  • An yi hasahen ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ka iya rashin nasara a zaben ranar Asabar 25 ga Fabrairu
  • Ridwan Oyafajo, masanin shari'a a Najeriya ne ya yi wannan hasashen bisa la'akari da rigingimun cikin gida da suka addabi PDP
  • Atiku na neman zama shugaban kasa karo na Shida kenan bayan rashin nasara a yunkuri 5 da ya yi a baya tun 1993

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha kashi sau biyar a yunkurinsa na hawa kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Wazirin Adamawa, wanda yanzu haka yake neman zama shugaban ƙasa a PDP, ya yi takarar hawa mulkin Najeriya a shekarun 1993, 2007, 20011, 2015 da 2019 amma bai samu nasara ba.

Atiku da Lauya Oyafajo.
Oyafajo ya yi hasashen rashin nasara ga Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Yadda Atiku ya nemi zama shugaban kasa a tarihi

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tsohon Minista Ya Bayyana Yankin Da Atiku Zai Lashe

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya shiga tseren karo na shida kenan kuma a wannan karo zai gwabza da tsohon makusancinsa, Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyar APC mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu, Ridwan Iyafajo, fitaccen lauya a Najeriya, yayin wata hira da Legit.ng Hausa, ya ce da yuwuwar tarihi ya maimaita kansa, Atiku ya ƙara rashin nasara a karo na Shida.

Lauyan ya shaida mana cewa mai yuwuwa Atiku ba zai kai labari ba a zaben ranar Asabar sakamakon rikicin cikin gida da ya mamaye jam'iyyarsa watau PDP.

PDP ta rasa zaman lafiya tsakanin 'ya'yanta tun bayan ayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Gwamnoni 5 suka ɓalle suka kafa tawagar da suka yi wa laƙabi da G-5, sun gindaya sharaɗin sai shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus kafin su marawa Atiku baya.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

Abinda zai iya faruwa da Atiku - Oyafajo

Da yake tsokacin kan halin da Atiku ya tsinci kansa a PDP, Oyefajo ya ce:

"Har yau jam'iyyarsa ba ta farfaɗo daga koma bayan da ta samu ba tun bayan gama zaɓen fidda gwani. Wasu mambobi ba su aminta da zabin abokin takararsa ba kuma sun sha alwashin janye goyon bayansu."
"Ɗan takarar yana da manufofi masu kyau kuma ya zagaye ƙasar nan yana tallata manufarsa amma don mutane sun saurari manufofinka ba zai sa ka lashe zabe ba."
"Wannan ɗan takara (Atiku) yana da magoya baya amma su kaɗai sun isa su kai shi ga nasara a zabe? Lokaci zai yi alƙalanci domin ko jihar da ya fito da wuya ya iya kai labari, bare ƙasa baki ɗaya."

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Rushe Tsari, Ta Koma Inuwar APC a Karamar Hukumar Jihar Borno

Kwanaki kalilan gabanin fafata zaben shugaban Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta kasa PDP ta gamu da cikas a arewa maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ta Karewa Atiku, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Arewa Kwana 5 Gabanin Zaben 2023

Shugabanni, mambobin da yan takara a karamar hukuma guda a jihar Borno sun fice daga PDP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel