Mahaifar Shugaban Kasa da Jihohi 3 da Aka Fi Yawan Wadanda Suka Karbi PVC
- Hukumar zabe na kasa ta ce akwai mutane 93,469,008 da suka yi rajistar yin zaben 2023 a Najeriya
- Alkaluman da INEC ta fitar sun nuna a cikin wannan adadin, mutane 87,209,007 sun karbi katinsu
- Har aka rufe kofa, kason wadanda ba su karbi katinsu na PVC da Hukumar ta buga, ba su kai 7% ba
Abuja – Ganin zaben 2023 ya zo, hukumar zabe na kasa watau INEC, ta tabbatar da cewa 93.3% na wadanda suka yi rajista suka karbi katin zabensu.
INEC tace katin zabe wanda aka fi sani da PVC ya shiga hannun mutane 87,209,007 a Najeriya.
A cikin mutum 93,469,008 da suka yi rajistar kada kuri’a a zabe mai zuwa, bayanan da aka samu daga wajen hukumar INEC ya nuna 93% sun yi dace.
Zuwa yanzu akwai PVC 6,259,229 da ba a karba ba, adadin yana wakiltar 6.7% na wadanda suka yi rajistar mallakar katin a lokacin da aka bude kofa.
Tun a ranar 5 ga watan Fubrairu aka dakatar da karbar katunan zabe bayan INEC ta bada damar karbar sababbin katin tun daga 12 ga watan Disamba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkaluman zaben 2023
Jihohin da ke kan gaba a wajen karbar wannan kati su ne Bauchi, Anambra da Katsina.
A bangaren jihohin da aka samu karancin wadanda suka karbi PVC akwai Osun, Oyo, Ogun, Ondo da Legas, dukkansu daga Kudu maso yammacin Najeriya.
Jihohin da aka karbi PVC sosai:
- Bauchi - 99%
- Anambra - 98.8%
- Katsina - 98.4%
Jihohin da ba aka karbi PVC sosai ba:
- Osun - 81.5%
- Oyo - 84.3%
- Ogun - 84.7%
- Edo - 85.1%
- Ondo - 86.9%
- Lagos – 88%
Inda za a fafata a 2023
A wani rahoto na musamman da muka fitar, kun ji takarar Shugaban Kasa za tayi zafi tsakanin jam’iyyun nan na APC, PDP, LP da NNPP a wasu Jihohi.
Za ayi gumurzu a Jihohin Kano da Kaduna, sannan a karon farko tun 1999, PDP tana fuskantar barazana a Ribas, kuma LP za ta kawo kalubale a Legas.
Asali: Legit.ng