Da Ya Sayar Da Mahaifinsa Mai Shekaru 82 Ga Matsafa Kan N1.8m A Ekiti

Da Ya Sayar Da Mahaifinsa Mai Shekaru 82 Ga Matsafa Kan N1.8m A Ekiti

  • Kotu ta tsare wani mutum bisa zargin hada kai da abokinsa tare da yin garkuwa da siyar da mahaifinsa ga matsafa
  • Dan sanda mai gabatar da kara ya karonto kunshin tuhuma tare da bayyana yadda aka siyar da dattijon mai shekaru 82 kan kudi naira miliyan 1.8
  • Alkalin kotun majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti ya aike da mutum uku da ake zargi, ciki harda dan marigayin zuwa gidan gyaran hali

Jihar Ekiti - Wata kotun majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti, ta aike da wasu mutum uku zuwa gidan gyaran hali a Ado-Ekiti, da ke Jihar Ekiti, bisa laifin garkuwa da wani dattijo mai shekaru 82, Michael Obasuyi, Daily Trust ta rahoto.

Alkalin kotun, Bankole Okuwasanmi, ya yi umarni da a tsare wanda ake zargi, Sunday Obasuyi (42), dan marigayin; Akinniyi (51) da Bobafe Sunday (51) har zuwa lokacin da zai ji shawarar daraktan karrarakin jama'a (DPP).

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Gudumar kotu
Kotu ta tsare wani mutum kan sayar da mahaifinsa ga matsafa a Ekiti. Hoto: The Cable
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, mai gabatar da kara, Sufeto Akinwale Oriyomi, ya shaidawa kotu cewa ana zargin wanda ake kara da garkuwa da wani dattijo ranar 1 ga watan Fabrairu, da misalin 11:00 na safe a Agbado-Ekiti, karamar hukumar Gboyin, kuma daga bisani, bayan satika, an tsinci gawarsa a cikin wani rami.

Mai gabatar da kara ya cigaba da cewa wanda ake zargi na daya, Obasuyi, ya hada kai da Akinniyi suka siyar da mahaifinsa kan kudi naira miliyan 1.8 ga wanda ake zargi na uku, Sunday, wanda shi ne boka.

Ya bayyana cewa laifukan sun saba da sashe na 280, 279 da 234 na kundin manyan laifukan Jihar Ekiti, 2021.

Masu Masu Satar Mutane Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda Yayinda Suke Kokarin Karbar Saura Kudin Fansa a Gombe

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

A baya kun ji cewa rundunar yan sanda a Jihar Gombe a ranar Talata ta gabatar da wani Salisu Saidu da Mohammad Aminu, wadanda aka cafke lokacin karban kudin fansa har N300,000 daga yan uwan wadanda suka sace.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda, Mahid Abubakar, ya ce hakan ya faru ne bayan tawagar masu garkuwar sun karbi N100,000 bayan sace wani Jibrin Muhammed a Taraba, kamar yadda Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164