Jerin Jihohi 6 da Za a Fafata da Gaske Tsakanin ‘Yan Takaran Shugaban Kasa

Jerin Jihohi 6 da Za a Fafata da Gaske Tsakanin ‘Yan Takaran Shugaban Kasa

  • Mutum fiye da miliyan 93 suka yi rajistar zaben da za a shirya a Jihohi 36 da Babban birnin Abuja
  • Masu nazarin siyasa sun ce zaben wannan karo ya sha bam-bam da sauran zabukan da aka yi a baya
  • ‘Yan takaran da ke kan gaba sun hada da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso

Abuja - A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro wasu jihohi da ake ganin za a kai ruwa-rana tsakanin ‘yan takaran kujerar shugaban kasa.

1. Bauchi

Siyasar Bauchi ta fita dabam a Najeriya, mu na ganin cewa jihar tana cikin inda za a gwabza musamman tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu.

Yayin da Gwamna Bala Mohammed yake tare da Atiku Abubakar, APC tana sa ran samu nasarar ‘dan takaranta, ta dogara da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Babban Abinda Ya Sa Atiku Abubakar Zai Iya Rashin Nasara a Zaben Ranar Asabar

A gefe guda, Rabiu Musa Kwankwaso yana tare da irinsu Halliru Jika, Hamma Misau. Peter Obi zai sa ran tsintar kuri’u a wasu yankunan da ke jihar.

2. Benuwai

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A Benuwai akwai yaki tsakanin Shugaban jam’iyya watau Dr. Iyorchia Ayu da Gwamna Samuel Ortom wanda yake neman zama Sanata a zaben 2023.

Duk da rikicin Atiku Abubakar da gwamna, yana tare da sauran Sanatoci da manyan ‘yan siyasar jihar. Ortom yana goyon bayan takarar Peter Obi a LP.

Ana ganin APC za ta dogara da irinsu George Akume wanda mai gidan Gwamna ne, Ministan zai yaki PDP a yankin Arewa maso yammacin Benuwai.

Kwankwaso
Tinubu tare da Kwankwaso a Abuja Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

3. Kaduna

A hasashenmu Kaduna ta na cikin jihohin da kusan duka manyan ‘yan takaran za su samu kuri’a. Gwamna Nasir El-Rufai zai dage sosai a kan nasarar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ba na Goyon Bayan Tinubu Inji Daya Daga cikin Gwamnonin PDP da ke Fada da Atiku

Atiku Abubakar zai dogara da ‘dan takarar Gwamnan Kaduna, Isa Ashiru Kudan da Mai gidansa Sanata Ahmad Makarfi da sauran kusoshin jam’iyyar PDP na jihar.

Akwai yiwuwar Peter Obi ya samu kuri’un kudancin Kaduna da ma’aikata a yankin Zaria a yayin da jam’iyyar NNPP za ta ci buri daga masoyan Rabiu Kwankwaso.

4. Kano

Malaman jihar Kano sun rabu tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa da ‘dan takaran APC wanda yake sa ran samun gudumuwa daga wajen Gwamna mai-ci.

Atiku yana tare da Ibrahim Shekarau, Aminu Wali, Ibrahim Little da sauran jiga-jigan PDP a Kano. Zaben na 2023 zai nuna karfin Ganduje, Shekarau da Kwankwaso.

Akwai yiwuwar Peter Obi ya samu kuri’un kudancin Kaduna da ma’aikata a yankin Zaria. Jam’iyyar NNPP ta na tsammanin samun kuri'un masoyan Kwankwaso.

5. Lagos

Legas ta na cikin jihohin da Legit.ng Hausa ta ke ganin za a gwabza a zaben bana. Tun 1999, ‘dan takaran jam’iyyar APC, Bola Tinubu yake da ta-cewa a siyasarta.

Kara karanta wannan

Zabe Ya Gabato, IGP ya yi Mamaya da Wasu Sauye-sauyen Kwamishinoni a Manyan Jihohi

Masu nazari su na ganin nasarar APC musamman a kauyukan Kudu maso yamma, amma ba abin mamaki ba ne kuri'un bare su yi tasiri a Legas a zaben Asabar.

Obi yana ganin yana da masoyan da za su kawo masa kuri'u a tsohon birnin tarayyar. Idan PDP tayi rashin sa'a, rikicin cikin gidanta zai batawa a Atiku lissafi a nan.

6. Ribas

Alamu sun nuna za a fafata a jihar Ribas musamman ganin yadda mutanen Gwamna Nyesom Wike suke goyon bayan mulki ya zauna a hannun jam’iyyar APC mai-ci.

Atiku Abubakar da mutanensa su na shan wahala wajen tallata jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa. Babu mamaki rikicinsu Nyesom Wike da Atiku ya yi tasiri.

The Africa Report ta ce za a fafara a jihar Kudu maso kudancin kasar musamman ganin yadda matasa suke goyon bayan Obi mai neman takara a jam’iyyar LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel