Layuka Sun Ragu: Bankuna Zasu Kara Adadin Yawan Kudin da Mutane Zasu Cire Daga ATM

Layuka Sun Ragu: Bankuna Zasu Kara Adadin Yawan Kudin da Mutane Zasu Cire Daga ATM

  • Bankuna a Najeriya na yunkurin kara adadin kudin da za’a iya cirewa
  • Wannan yana nufin Bankunan zasu kara adadin da zai zarce umarnin da CBN ta bayar
  • Hakan na zuwa ne bayan CBN ya saki biliyoyin nairori domin su zagaya cikin kasa, hakan yasa layuka a bankuna

Da alama dai matsalar rashin kudin kashewa ya soma zuwa karshe, a yayin da aka samu karancin layuka dake godon kokarin samun kudin da mutane zasu kashe da ake kira da “Cash” a harshen bature mai jan kunne.

Domin kuwa rahotanni na nuni da cewar Bankunan kasuwanci a Najeriya na kokarin kara adadin kudin da masu hulda dasu zasu iya cirewa daga:

N20, 000 zuwa N50, 000

N80, 000 zuwa N100, 000.

Bank queue
Kwastomomin Banki Sun Hau Layi Domin Cire Kudi Cash Hoto: PATRICK MEINHARDT / Gudunmawa
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

Wannan gagarumin yunkurin na zuwa ne, a cewar bankunan domin rage cunkoson da ake samu a jikin injinan dake fitar da kudi na ATM.

Bugu da kari, a cewar Jaridar Legit.ng wannan yunkuri na zuwa ne a wani salon kokari da bankunan ke yi domin ganin sun rage cunkoson da ake dashi a cikin dakunan hada-hadar dake a cikin manya manyan biranen kasar nan.

CBN ta Taki Biliyoyin Nairori Cikin Kasa Suna Zagayawa

A wani labarin makamancin wannan kuma, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya Umarci bankunan kasuwanci a ranar juma’a 24 ga watan Maris 2023, akan su biya bashin kudaden da aka nema su biya na cash domin rage rashin kudin kashewa na zahiri da yayi katutu a hannun mutane.

Wata majiya daga cikin bankunan, suna fadin cewa, bankunan na kokarin kara adadin kudi daga N20, 000 zuwa 50,000 da kuma daga N80, 000 zuwa N100, 000.

Kara karanta wannan

Mata Sun Yi Zanga-Zanga Zindir Kan Zaben Najeriya a Ofishin Jakadancin Amurka a Ramadan

Dalilin yin hakan ance yana da nasabar rage yawan layi da yayi katutu a bankunan da injinan ATMS dake lungu da sakon sakar nan.

Najeriya dai na fama da karancin kudin kashewa na zahiri tun bayan canja fasalin kudin da babban bankin kasar (CBN) yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel