'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam'iyar APGA Na Gunduma a Ebonyi

'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam'iyar APGA Na Gunduma a Ebonyi

  • Kwana kaɗan kafin zabe, yan ta'adda sun kashe shugaban APGA na gunduma a jihar Ebonyi, kudu maso gabashin Najeriya
  • Wani ɗan uwan mamacin ya ce lamarin da ɗaga hankali ganin yadda suka fito da shi yana cikin bacci jiya da daddare
  • Wani masoyin jam'iyyar APGA ya ce marigayi Idoko mutun ne nai neman na kansa da kokarin taimaka wa al'umma

Ebonyi - Wasu yan bindiga da ba'a sani ba sun halaka shugaban jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) na gudumar Ohofia Agba, Mista Monday Idoko, a karamar hukumar Ishielu, jihar Ebonyi.

Jaridar Vanguard ta ce maharan sun harbe shi a tsakiyar ka a mahaifarsa ƙauyen Onueke, yankin Ohofia-Agba da misalin karfe 11 na daren jiya Laraba.

Taswirar jihar Ebonyi.
'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam'iyar APGA Na Gunduma a Ebonyi Hoto: vanguard
Asali: UGC

Wani ɗan uwan Mamacin, wanda ya yi magana cikin hawayen bakin ciki kuma ya nemi a sakaya bayanansa, shi ne ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ta wayar salula.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Babban Abinda Ya Sa Atiku Abubakar Zai Iya Rashin Nasara a Zaben Ranar Asabar

Ya ce makasan sun kutsa cikin kauyen kana suka zakulo shugaban jam'iyyar wanda ya riga ya fara bacci, suka harbe shi a kai, nan take rai ya yi halinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Ɗan uwana, labarin akwai tashin hankali, wani ɗan gidanmu ya sanar da ni cewa wasu mutane ɗauke da bindigu suka kutsa gidan da suke kwance kafin dare ya raba."
"Suka fito da ɗan uwana daga bisani suka bindige shi a kai, sun yi kokarin garzayawa da shi Asibiti amma rai ya yi halinsa tun a cikin kauyen. Muna cikin yanayin jimami tun jiya."

Wani mamban APGA wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce marigayi Idoko ya maida hankali wajen shirye-shiryen zuwa ɗan takarar gwamnan APGA, Benard Odoh, kafin a kashe shi.

Ya ayyana marigayin da mutum mai dogaro da kai wanda ya sadaukar da komai nasa domin ci gaban jam'iyyar APGA da al'ummar yankinsa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 2 Zabe, Yan Daba Sun Bude Wa Shugaban Majalisar Dokoki Wuta Yana Tsaka da Taro

Mahara sun farmaki ayarin ɗan takarar PDP

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar PDP a Enugu, Sun Kashe Direba

Wasu yan ta'adda ba'a san manufarsu ba sun kai hari kan ayarin tawagar kamfen ɗan takarar majalisar tarayya daga jihar Enugu ana dab da babban zabe ranar Asabar.

Lamarin dai ya faru awanni bayan an kashe ɗan takarar Sanatan Enugu ta gabas na jam'iyyar LP ranar Laraba da yammaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262