Atiku, Tinubu Da Wasu Yan Takara Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Atiku, Tinubu Da Wasu Yan Takara Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

  • Ana kwana uku zaben shugaban kasa na Najeriya, wasu cikin yan takarar shugaban kasar sun halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
  • Daga cikin wadanda suka halarci taron da aka yi a ranar Laraba a Abuja akwai Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na jam'iyyar APC da takwararsa Alhaji Atiku Abubakar na APC
  • Duk da cewa halarton taron saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyan ba wajibi bane, yana da muhimmanci wurin ganin an takaita rikici yayin zabe da bayan zabe

FCT, Abuja - Gabanin babban zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar, yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun siyasa a ranar Laraba sun taru a Abuja don rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya.

Wadanda suka halarci taron sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da takwararsa na Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Zafafan Hotunan Kamfen Tinubu/Shettima Na Karshe Da Ya Gudana a Legas

Yan takarar
Wasu cikin yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 na Najeriya. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta rahoto cewa yarjejeniyar zaman lafiyar ba wajibi bane ga jam'iyyun siyasa su rattaba hannu a kai. Amma dai wani mataki ne na taimakawa wurin kare afkuwar rikicin zabe.

A kalla yan takarar 18 ne suka neman gadon kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a don zama shugaban kasar bakar fata mafi yawan al'umma a duniya.

Tsohon shugaban Najeriya Dr Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga matasa da yan siyasa su yi zabe cikin lumana

A gefe guda, tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan shima ya yi kira ga yan siyasa da matasan Najeriya su yi zabe cikin zaman lafiya da lumana a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya yi wannan kiran ne cikin wata sanarwa da ofishinsa ta fitar a ranar Talata 21 ga watan Fabrairu, inda ya shawarci yan siyasa su rika kula da irin maganganun da suke furta wa.

Kara karanta wannan

Majalisar Malaman Kasar Yarbawa Sun Shirya Addu'a Ta Musamman Don Nasarar Tinubu

Har wa yau, Jonathan ya yi kira ga matasan Najeriya kada su yarda wani dan siyasa ya yi amfani da su wurin tada zaune tsaye yayin zaben yana mai cewa suna da damar zaben wanda zai gina musu kasa ta gari da za su yi alfahari da ita a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel