Majalisar Malaman Kasar Yarbawa Sun Shirya Addu'a Ta Musamman Don Nasarar Tinubu

Majalisar Malaman Kasar Yarbawa Sun Shirya Addu'a Ta Musamman Don Nasarar Tinubu

  • Wasu Malaman addinin Musulunci sun taru a Abuja don gudanar da addu'a na musamman kan zabe
  • Malaman dukka ya kabilar Yoruba sun ce bayan dogon zama da tattauna, sun zabi wanda zasu yi
  • Sun yi addu'ar Allah ya baiwa Asuwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC nasara a zaben ranar 25 ga wata

Abuja - Kungiyar Malaman Addinin Musulunci na kasar Yarbawa Concerned Yoruba Muslim Scholars in Nigeria (CYMSN), ta bayyana cewa dan takarar shugaban kasan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bole Tinubu, ne zabin su.

Malaman sun shirya zaman addu'a na musamman don nasarar Tinubu a zaben da zai gudana nan da yan kwanaki da kuma a zabe cikin zaman lafiya da lumana.

An gudanar da taron addu'ar ne ranar Litinin a babban Masallacin tarayya dake birnin tarayya Abuja karkarshin jagoranicin Abdurrasheed Mayaleke, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Dab da zabe, Tinubu ya dura a jiharsu, zai yi wani taro da shugabannin Yarbawa

Scholrs
Majalisar Malaman Kasar Yarbawa Sun Shirya Addu'a Ta Musamman Don Nasarar Tinubu Hoto: TheCable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren kungiyar, Olaiya Abideen, ya bayyana cewa yan Najeriya zasu ji dadi idan Tinubu yayi nasara a zaben.

Ya ce:

"Mu kungiya ce mai aiki don samun zaman lafiya a zabe. Mun shirya wannan addu'a ne domin neman shafa'a gaban Allah ya bada zaman lafiya a zaben, saboda lamura sun ta'azzara a kasar."
"Wahalar man fetur da rikicin sauya fasalin Naira abubuwan ne na damuwa matuka. Mun taru ne a nan don addu'ar Allah ya kawo mana mafita don muyi zabe cikin kwanciyar hankali."
"Hakazalika muna addu'ar nasarar Asiwaju da Shettima. Al'ummar Musulmi ta zauna lokuta da dama kuma mun yanke shawarar mara goyon baya da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima."

Ya yi kira ga yan Najeriya da yan Najeriya su guji abubuwan da zasu iya haddasa rigima lokacin zaben.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

Jam'iyyar APC ta ce 'yan Najeriya su natsu su zabi Tinubu, ta fadi dalilanta

A wani labarin kuwa, jam’iyyar All Progressives Congress (APC), APC ta baiwa yan Najeriya shawarar cewa su dage su zabi dan takararta Asiwaju Bola Tinubu a zaben da zai gudana nan da yan kwanaki.

Mr. Isaack Kekemeke, mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyyar kudu maso yamma ya bayyana hakan a wani jawabin da ya gabatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel