"Har Yanzu Nine Sahihin Ɗan Takarar PDP", Sanata Nnamani Ya Magantu

"Har Yanzu Nine Sahihin Ɗan Takarar PDP", Sanata Nnamani Ya Magantu

  • Sanatan PDP kuma ɗan takara a zaɓen ranar Asabar ya fito yayi ƙarin haske kan takarar sa
  • Chimaroke Nnamani yace har yanzu shine sahihin ɗan takarar jam'iyyar duk da korar da aka yi masa
  • Ya tabbatar da cewa zai cigaba da wakiltar mutanen yankin sa yadda ya dace a majalisar dattawa

Enugu- Tsohon gwamnan jihar Enugu kuma sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas a majalisar dattawa, Dr. Chimaroke Nnamani, ya gayawa mutanen mazaɓar sa da su fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su suyi masa ruwan ƙuri'u a zaɓen ranar Asabar.

Idan ba a manta da ba dai jam'iyyar PDP ta kori Nnamani daga cikinta, hukuncin da sanatan ya ƙi amimcewa da shi kuma ya ƙalubalanta. Rahoton Leadership

Nnamani
Har Yanzu Nine Sahihin Ɗan Takarar PDP -Sanata Nnamani Ya Magantu Hoto: Punch
Asali: UGC

Sai dai a wata sanarwa a jiya Talata, Nnamani ya tabbatar da cewa takarar sanatan da yake yi bata fuskantar wata barazana ko tangarɗa inda ya ƙara da cewa lallai wannan kujerar tasa ce.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Ɗau Zafi: Kwana 4 Gabanin Zabe, Jam'iyyar PDP Ta Kori Ɗan Takarar Gwamna Kan Laifi 1

Ya gayawa mutanen sa da suyi watsi da duk wani abu saɓanin hakan inda ya tabbatar musu da cewa yana da cikakken shiri domin tunkarar zaɓen na ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nnamani ya kuma tabbatar wa da mutanen sa cewa zai cigaba da yi musu ingantaccen wakilci a majalisar dattawa, inda ya ƙara da cewa za su kwashi romon dimokuraɗiyya.

Ya kuma ƙara da cewa zai yi gaskiya da adalci inda yake cewa zai yi bakin ƙoƙarin sa wajen share duk wani kukan su a majalisar. Rahoton Punch

Nnamani ya kuma roƙi mutanen sa da su zama masu bin doka da oda inda ya tunatar da su kan su yi zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Zabe Saura ‘Yan Kwanaki, Jam’iyyar NNPP ta Gano ba ta da ‘Dan Takarar Sanata a Kano

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano, ta gano bata da ɗan takarar sanata ana saura kwanaki kaɗan a fara kaɗa ƙuri'a.

Sunan ɗan takarar sanatan na jam'iyyar NNPP baya daga cikin jerin sunayen ƴan takarar da zasu fafata zaɓe wanda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel