Rikicin PDP Ya Munana, Gwamnan Arewa Ya Shirya Yafe Takararsa Saboda a Doke Atiku
- Idan ta kama Samuel Ortom ya fadi zaben Sanata saboda Peter Obi, a shirya yake ya yi hakan
- Gwamnan Benuwai bai damu Jam’iyyar PDP ta sha kasa idan dai Obi zai zama shugaban kasa ba
- Ortom ya ce ba a maganar APC, PDP ko wata Jam’iyya a 2023, ya fadawa Ibo su goyi bayan LP
Benue - Gwamnan jihar Benuwai ya ce ya shirya hakura da takarar da yake yi a zabe mai zuwa domin ganin Peter Obi ya zama shugaban Najeriya.
Samuel Ortom ya na neman kujerar Sanatan Benuwai ta Arewa maso yamma a Majalisar Dattawa, The Cable ta rahoto ya ce zai iya yafe takarar.
Da yake zantawa da Ibo a jihar Benuwai, an rahoto Ortom yana cewa lokaci ya yi da mulki zai fada hannun mutumin Kudu maso gabashin kasar nan.
Gwamnan ya fadawa ‘yan kabilar ta Ibo cewa bai kamata su yi wasa da damar zaben LP ba.
Jawabin Samuel Ortom
“A wurina ba a maganar ina yin takara. Kwarai, mutanen jihar Benuwai sun sayo mani fam, na kuma zagaya domin yin kamfe, sun yarda za su zabe ni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma idan ta kama in sadaukar da burin zama Sanatana saboda Peter Obi ya yi nasara, shikenan an gama.
Na san idan akwai wasu kabilu a Duniya da suke da hadin-kai, su ne Ibo. Wannan dama ce da ku ka samu domin 'Dan Kudu maso gabas ya yi mulki.”
- Samuel Ortom
Sahara Reporters ta rahoto Gwamnan yana cewa lamarin takarar Obi ba maganar jam’iyya ba ne, an ajiye batun APC, PDP ko SDP, ana duba kishin kasa.
Me kuma ku ke nema?
Mista Ortom yake cewa idan ya ji wani Ibo yana sukar ‘dan takaran na LP, sai ya rasa manufarsa, domin su ne ke kukan an maida mutanensu saniyar ware.
A jawabinsa Ortom ya ce wani malaminsa ya fada masa Obi zai karbi mulkin Najeriya, ya ce mutanen Benuwai sun yi masa mubaya'a a zaben bana.
"Ba ku ke kukan ba ayi da ku tun ba yakin yakin Biyafara ba – Dama ta samu a zabi Peter Obi."
- Samuel Ortom
2023 sai Obi - Mai girma Samuel Ortom
Ba boyayyen labari ba ne cewa Gwamnan Benuwai yana cikin ‘Yan G5 da ke yakar takarar Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP saboda a dalilin sabaninsu.
A baya Ortom ya nuna Peter Obi yake goyon baya ya zama shugaban Najeriya a Mayun 2023 a maimakon ‘dan takaransu da jam'iyyar PDP ta tsaida.
Asali: Legit.ng