Wani Mutum Dan Tsurut Ya Isa Filin Gangamin Kamfen Din Tinubu a Legas, Bidiyonsa Ya Yadu

Wani Mutum Dan Tsurut Ya Isa Filin Gangamin Kamfen Din Tinubu a Legas, Bidiyonsa Ya Yadu

  • Wani mutum mai karamin jiki ya isa filin gangamin kamfen din Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC a Legas
  • Mutumin dan tsurut da shi ya ja hankalin mutane da dama da suka hango shi yana tafiya a kan hanya
  • Bawan Allan ya bayyana sunansa a matsayin Muhammadu Buhari yayin da ya tsaya cikin salo domin a dauke shi hoto

Jama'a sun yi cece-kuce bayan cin karo da bidiyon wani mutum dan tsurut da aka ganio a wajen gangamin kamfen din Bola Tinubu na jihar Legas.

An gano mutumin yana tafiya cike da kwarin gwiwa yayin da mutanen da ke wajen suka lura da shi cikin kankanin lokaci saboda yanayin surar jikinsa.

Mutum mai karamin jiki
Wani Mutum Dan Tsurut Ya Isa Filin Gangamin Kamfen Din Tinubu a Legas, Bidiyonsa Ya Yadu Hoto: @thenationnewspaper
Asali: Instagram

A wani bidiyo da jaridar The Nation ta wallafa a Instagram, mutumin ya bayyana sunansa a matsayin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Kwandastan Mota Ya Koma Yawo Da POS Saboda Fasinjojin Da Basu Da Tsaba a Hannu Ya Ba Da Mamaki

An gano wani mutum dan tsurut a wajen kamfen din Tinubu

Yana tafiya klan hanyar da ya cika da sauran magoya bayan dan takarar shugaban kasar na APC lokacin da mai daukar kamara ya hango shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin na sanye da riga da aka yi wa ado da sunan jam'iyyar yayin da yake tafiya a filin taron cike da alfahari.

Ya yi tsayuwa iri-iri yayin daukar hotuna yayin da ya bayyana sunansa. Bidiyon ya haifar da martani tsakanin masu amfani da Instagram.

Jama'a sun yi martani

@centchris_ ya ce:

"Daga ina kuka siyo wannan."

#iam_skaydors1 ya yi martani:

"Da wannan halin da kake ciki shine kuma kake goyon bayan APC wahala bata isarka ne nkubi?

@prolificemma10 ya ce:

"Wahala bata isarka ne."

@kweenchygor30 ya ce:

"Ba zai yi tashe ba. Sai su sake wasu dabarun."

Kara karanta wannan

Ka Kadde: Bidiyon Yadda Aka Kama Wani Mutum Dauke Da Sabbin 'Yan N500 Na Bogi, Jama'a Sun Girgiza

Matashiya yar Najeriya ta dawo daga Turai don yin zabe

A wani labarin kuma, wata matashiya yar Najeriya da ke zaune a Turai ta dawo gida Najeriya domin sauke hakkinta na yar kasa a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Matashiyar wacce ta bayyana cewa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC za ta zaba domin ya zama magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce yayarta ta yi mamakin ganinta.

Moore ta ce ta sanar da yayar tata cewa tana nan zuwa kasar amma sai ta zata wasa take yi har sai da ta yi ido hudu da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel