Shugaban Kasa a 2023: “Na Dawo Najeriya Don Na Zabi Tinubu” – Matashiya Mazauniyar Turai

Shugaban Kasa a 2023: “Na Dawo Najeriya Don Na Zabi Tinubu” – Matashiya Mazauniyar Turai

  • Wasu yan Najeriya mazauna kasar waje basa son ayi babu su wajen zabar sabuwar gwamnati da za a yi nan da yan kwanaki kadan
  • Wata matashiya da ke zaune a Turai ta garzaya shafinta na Twitter don bayyana cewaza ta dawo Najeriya domin ta kada kuri'arta da goyon bayan Bola Tinubu
  • Matashiyar mai suna Moore wacce ta wallafa hoton katin zabenta ta bayyana cewa ta dawo kasar ne don sauke hakkin da ya rataya a wuyanta

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wata mai amfani da Twitter mai suna Moore ta ce ta dawo Najeriya don zabar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress(APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Moore, mai bayar da shawarwari kan tafiye-tafiye, ta tuna yadda ta sanar da yar'uwarta shawarar da ta yanke na dawowa Najeriya don sauke hakkinta na yan kasa da kuma aiwatar da wani aikin.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Najeriya sun gaji da Buhari, matar Atiku ta yi bayanai masu daukar hankali

Bola Tinubu
Shugaban Kasa a 2023: “Na Dawo Najeriya Don Na Zabi Tinubu” – Matashiya Mazauniyar Turai Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ta dawo Najeriya da katin zabenta, yar'uwarta ta sha mamaki

A cewar Moore, yar'uwar tata ta kadu da ganin isowarta kasar domin a zatonta wasa kawai take yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Moore ta wallafa hotonta a filin jirgin sama, inda ta nunawa duniya katin zabenta.

Ta wallafa:

"Na fada ma yar'uwata zan zo na yi zabe da kuma kammala duk wasu ayyuka da ke jirana, ta zata wasa nake yi.
"A ranar 20 ga wata na dauki jakata da katin zabena, na isa Najriya lafiya. BOLA AHMED TINUBU zan zaba da izinin Allah."

Tinubu na gudanar da gangamin kamfen dinsa na karshe a Lagas

A wani labarin, mun ji cewa a yau Talata, 21 ga watan Fabrairu ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi gangamin yakin neman zabensa na karshe a jihar Lagas.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hadimar Aisha Buhari ta tafi kotu, ta ce matar Buhari ta ci zarafinta, a bata diyyar N100m

Ana sanya ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance a wajen kamfen din, inda zai yi jagoranci ga daukacin gwamnonin da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar mai mulki da sauran masu ruwa da tsaki a taron.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da babban zaben kasar inda za a fara da zaben shugaban kasa tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel