Yan Bindiga Sun Jefa Bam Ofishin Yan Sanda, Sun Hallaka Jami'ai 3

Yan Bindiga Sun Jefa Bam Ofishin Yan Sanda, Sun Hallaka Jami'ai 3

  • Ana saura mako guda zabe wasu yan bindiga dadi sun kai hari ofishin yan sanda a jihar Anambra
  • Rahotanni sun nuna cewa an jefa Bam cikin ofishin yan sandan sannan aka bude musu wuta
  • Akalla jami'an yan sanda uku ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan mumunan hari

Ana saura kasa da mako guda zaben shugaban kasa an 2023, wasu yan bindiga sun kuma kai hari ofishin yan sanda a jihar Anambra, Kudu maso gabashin Najeriya.

Jihar Anambra ce mahaifar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Gregory Obi.

Wakilin Legit dake Anambra, Mokwugwo Solomon, ya bayyana cewa an kai wannan hari ne da sanyin safiyar Asabar, 18 ga watan Febrairu, 2023 ofishin yan sanda dake unguwar Ogidi, karamar hukumar Idemili North.

A cewarsa akalla jami'an yan sandan uku ne suka ce ga garinku.

Kara karanta wannan

Manya Alkawura 3 Da Nike Yiwa Yan Najeriya Idan Na Zama Shugaban Kasa, Kwankwaso

Alkali
Babban Sifeton Hukumar yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da harin a jawabin da ya fitar.

A cewarsa:

"Hukumar yan sandan jihar Anambra ta tura karin jami'an tsaro karamar hukumar Idemili North biyo bayan garin da aka kai ofishin Ogidi da safiyar Asabar, 18/2/2023 inda jami'an yan sanda uku suka rigamu gidan gaskiya."
"Yan bindigan sun fara harbin kai mai uwa da wabi yayinda suke shiga cikin ofishin yan sandan kuma suka fara jefa bama-bamai, hakan ya basu damar shiga."
"Hukumar ta na Alla-wadai kan yadda aka rasa rayuka sakamakon wannan hari, amma tana kira ga jama'a su kwantar da hankulansu yayinda take kokarin dakile wadannan batagari."

Saura mako daya zabe

Tun shekarar da ta gabata, yan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB tana kai hare-hare ofishohin yan sanda da hukumar zabe ta INEC.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Saura kiris zabe, 'yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sanda, an kashe 3 daga cikinsu

Fusatattun matasan sun lashi takobin cewa ba za'a gudanar da zabe a gaba daya yankin kudu maso gabas ba.

Hukumar INEC dai ta bayyana cewa idan aka cigaba da kai wadannan hare-hare ofishinta za'a iya samun mushkila da zabe a yankin.

Masu ruwa da tsaki sun yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saki shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, la'alla wadannan hare-hare suyi sauki.

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya bayyanawa shugaba Buhari cewa a bashi amanar Nnamdi Kanu, idan aka sakeshi ba zai sake guduwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel