Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Tafi Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne

Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Tafi Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne

  • Bashir Ahmad, mashawarcin shugaban kasa kan sadarwa ta zamani ya yi wa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ba'a kan sukar sauyin naira
  • Gwamna Ganduje, cikin wani sautin murya da ya bazu a kafafen watsa labarai ya soki sauyin yana mai cewa wani mataki ne na kawo wa demokradiyya cikas
  • Amma Bashir, a bangarensa ya fada wa Ganduje ya tafi babban bankin kasa CBN ya kai kudinsa idan na halas ne daga bisani zai ji alert

Mashawarci na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan sadarwa na zamani, Malam Bashir Ahmad ya bukaci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya kai tsaffin takardun nairansa babban bankin kasa, CBN, idan na halas ne.

Ahmad ya mayar da martani ne ga Ganduje kan sukar sauya fasalin takardun naira da ya yi na cewa wani mataki ne kawo matsala ga demokradiyya da katsalandan ga babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

An Yi Dirama Yayin Da Wani Ya Taho Ofishin CBN Na Kano Dauke Na Tsaffin Kudi N50m Cikin Buhu, Bidiyon Ya Bazu

Bashir Ahmad
Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya kuma zargi Buhari da gabatar da tsarin daf da zabe, yana mai cewa ya kamata a yi hakan ne cikin shekaru bakwai da rabi da suka gabata ko bayan zabe.

Amma, a martanin da ya yi da Ganduje da wasu, Ahmad ya ce su dena surutu kuma su dauki tsaffin nairan su su kai CBN.

Ya ce:

"Da dama daga cikin jama'a suna tunanin cewa wannan kumfar bakin don kwato musu hakki ake yin ta, sai dai gaskiyar magana shi ne suna yi ne don kudaden da suka tara da ba za su iya kaiwa CBN ba, domin sun san akwai EFCC da NFIU sun zura na mujiya tare da saurare."

Ya kuma amsa Ganduje cikin ba'a yana cewa:

"Baba Buhari kuma na ce Habu na Habu ya ce a fadawa Baba Dan Audu idan kudaden da sike ta kumfar baki a kai na halak ne to su tattara su kai CBN, idan EFCC da NFIU sun tabbatar da sahihancin su shi kenan za su ji alat."

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Tona Abin da Ya Jawo Manya Suke Adawa da Tsarin Canza Nairori

A kan zargin da Ganduje ya yi na cewa Buhari na kokarin kawo cikas ga demokradiyya, Bashir ya ce:

"Ban tabbatar da cewa demokradiyya ta lalace ba, sai ranar primary election din da na yi takara, kirikiri aka aiko da daga sama aka yi mana murdiya a bainar jama'a, wai kawai saboda mu yan siyasar Abuja ne."

An kwashi yan kallo yayin da wani ya tafi CBN mayar da tsaffin naira miliyan 50

A wani rahoton kun ji cewa an kwashi yan kallo yayin da wani mutum ya tafi mayar da tsaffin kudi babban bankin kasa, CBN, cikin buhuna.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, mutumin ya ce shi dan kasuwa ne mazaunin Kano kuma yana sana'ar sayar da fulawa ne ga yan sari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel