2023: An Nemi Wike An Rasa Yayin da Atiku Ya Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP Na Ribaa

2023: An Nemi Wike An Rasa Yayin da Atiku Ya Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP Na Ribaa

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gana da jiga-jigan PDP na jihar Ribas a Abuja ranar Lahadi
  • Uche Secondus, tsohon shugaban PDP na ƙasa da tsohon gwamnan Ribas sun halarci wurin amma banda gwamna Wike
  • Atiku ya zauna da kusoshin ne a madadin ralin PDP na Ribas da ya soke domin gudun abinda ka iya zuwa ya dawo

Abuja - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyar PDP, Atiku Abubakar, ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar Ribas a babban birnin tarayya Abuja da yammacin ranar Lahadi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron daga Ribas har da tsohon shugaban PDP, Uche Secondus, Sanata Ben Bruce, tsohon gwamnan jihar, Celestine Omehia, da sauransu.

Atiku Abubakar.
2023: An Nemi Wike An Rasa Yayin da Atiku Ya Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP Na Ribas Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Meyasa Atiku ya kira taron?

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Atiku ya ce ya gana da masu ruwa na tsaki na Ribas ne domin ƙara basu hakuri da faɗa masu abinda ya sa aka soke rali a jihar.

Kara karanta wannan

"Kana Jawo Kama Tashin Hankali" Gwamna Wike Ya Ɗau Zafi, Ya Aike da Sako Ga Buhari da Atiku Kan Sabbin Naira

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na gana da masu ruwa da tsakin Ribas a Abuja jiya da dare, mun tattauna dalilin soke ralin kamfe na jihar, burina bai kai darajar jinin mutum ɗaya ba.

"Na faɗa musu ko bayan zabe mutanen Ribas na nan a cikin zuciyata," inji Atiku a shafinsa.

Kakakin kwamitin kamfen Atiku, Sanata Dino Melaye, ya ce sun shirya zaman ne a madadin ralin kamfen PDP na Ribas, wanda aka soke saboda abinda ka iya zuwa ya dawo.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka haɗa taron, Sanata Lee Maeba, ya tabbatar da cewa PDP zata samu galaba a jihar Ribas, kana ya lissafo ayyukan da suke fatan Atiku ya yi masu idan ya ci zaɓe.

Sai dai taron wanda ya gudana kwanaki kaɗan kafin zaɓe, an nemi gwamna Nyeosom Wike an rasa kuma ana ganin hakan na da alaƙa da rikicin cikin gida a PDP.

Kara karanta wannan

Kaico: Jinkirin 'alert' yasa ikitoci sun ki kula mata mai juna biyu, sun barta ta mutu a Kano

Atiku ya ɗaukarwa Ribas alƙawari

A nasa jawabin, ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku ya yi alƙawarin kammala aikin hanyar gabas maso yamma kuma zai dawo da shirin jin ƙai da afuwa na FG da zaran ya hau mulki.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bayan nan, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya wuce kai tsaye zuwa wani taron na daban da 'yan takarar majalisar tarayya na PDP.

Abokin takararsa kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ne ya yi jawabi ga yan takarar, inda ya bukaci su ci gaba da kamfe a mazaɓunsu na tarayya da Sanatoci.

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Dira Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10

Tsohon gwamnan Legas kuma ɗan takarar shugaban kasa na APC a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya halarci zaman gwamnonin ci gaba da NWC da ya gudana a Abuja.

Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne ya jagorancin kiran taron kan halin da ƙasa ta tsinci kanta na karancin naira.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Kara Shiga Tasku, Gwamnan PDP Ya Yanke Shawara Ta Karshe Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel