Rikici Tsakanin Fadar Shugaban kasa da Gwamnoni: APC Ta Kira Zaman Gaggawa Da Gwamnoninta

Rikici Tsakanin Fadar Shugaban kasa da Gwamnoni: APC Ta Kira Zaman Gaggawa Da Gwamnoninta

  • Shugaban jam'iyyar APC ya gayyaci gwamnonin jam'iyyar zama ana saura mako guda zabe
  • Rikicin dake gudana tsakanin wasu gwamnoni da fadar shugaban kasa na kara tsamari
  • Gwamnonin Kaduna, Jigawa, da Legas sun yi Alla-wadai da sabawa umurnin kotu da Buhari ke yi

Abuja - Uwar Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta kira zaman gaggawa da gwamnonin jam'iyyar yayinda ake sauran mako guda zaben shugaban kasa.

Zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya zai gudana ranar 25 ga watan Febrairu, 2023.

Shugaban uwar jam'iyyar, Abdullahi Adamu, ne ya kira zaman kuma Sakataren yada labaran jam'iyyar, Felix Morka ya sanar.

Abdullahi
Rikici Tsakanin Fadar Shugaban kasa da Gwamnoni: APC Ta Kira Zaman Gaggawa Da Gwamnoninta
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar a shafin jam'iyyar na Tuwita.

Yace:

Kara karanta wannan

PDP Yaudara Ce: Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Ce Ya Yi Murabus

"Shugaban uwar jam'iyyar All Orogressives Congress APC, Mai Girma Sanata Abdullahi Adamu, na kgayyatar gwamnonin jam'iyyar zuwa zaman gaggawa da za'ayi ranar Lahadi, 19 ga Febrairu, 2023 misalin karfe 2 a Sakatariyar jam'iyya dake Abuja."

Gwamnonin Kaduna, Legas da Jigawa Sun Bijire Wa Umurnin Buhari, Na Kano Ya Caccaki Shugaban Kasan

Akalla gwamnonin jam'iyyar APC uku sun fadawa al'ummarsu su yi watsi da umurin shugaba Buhari kuma su cigaba da amfani da tsaffin kudadensu na N500 da N1000.

Gwamnonin sun ce jama'a su cigaba da amfani da kudadensu har sai kotun koli ta yanke hukunci kan lamarin a ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.

Wannan ya biyo bayan jawabin da shugaba Buhari yayi da safiyar Alhamis kafin shillawa kasar waje.

A cewar gwamonin, hukuncin kotun koli ya fi karfin shugaba Buhari da kansa kuma wajibi ne kowa ya girmama doka komin girmansa.

Zaku tuna cewa wasu gwamnonin APC sun shigar da Buhari kotun da kimanin gwamnoni goma sukayi.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Kara Shiga Tasku, Gwamnan PDP Ya Yanke Shawara Ta Karshe Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

Gwamnonin sun hada da na Kaduna, Nasir El-Rufa'i; Na Kogi Yahaya Bello; Na Zamfara Muhammadu Bello Matawalle; dss.

Jawabin Ganduje

Wani faifan jawabi ya bayyana inda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ke caccakan Shugaba Buhari.

A hirar da yayi da Express Rediyo, an ji Ganduje na cewa Buhari na shirin rusa demokradiyya bayan shan moriyarta.

Yace abinda shugaban kasan ke yi da gayya ne don jam'iyyar APC ta fadi zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel