EFCC Ta Fadi Gaskiya Kan Rahoton Kai Samame Gidan Tinubu Ta Gano Biliyan N400bn
- EFCC ta yi karin haske kan rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa jami'anta sun kai samame gidan Tinubu
- Rahoton ya yi ikirarin cewa shugaba Buhari ne ya basu umarni kuma sun gano sabbin naira N400bn a gidan
- A sanarwan da EFCC ta fitar tace rahoton ƙanzon kurege ne domin ko kaɗan haka ba ta faru ba
Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arazikin kasa ta'adi (EFCC) ta musanta rahoton dake yawo a soshiyal midiya cewa jami'anta sun kai samame gidan Bola Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa EFCC ta ƙaryata rahoton wanda ya yi ikirarin cewa jami'anta sun gano biliyan N400bn a gidan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC.
Mai magana da yawun hukumar EFCC ta ƙasa, Wilson Uwujaren, shi ne ya musanta rahoton a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 19 ga watan Fabrairu.
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari
Me rahoton da ake yaɗawa ya kunsa?
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa rahoton dake yawo ya yi ikirarin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci EFCC ta kai samame gidan Tinubu kuma bisa sa'a ta zakulo sabbin kuɗi N400bn a ƙarƙashin kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene gaskiyar labarin?
Amma hukumar yaki da cin hanci da rashawa, a sanarwan da ta yi wa taken, "Bamu kai samame gidan Tinubu ba," EFCC ta ce ko kaɗan jami'anta ba su aiwatar da haka ba.
A ruwayar Vangaurd, Sanarwan ta ce:
"An awo hankalin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) kan rahoton dake yawo a soshiyal midiya cewa dakarunta sun kai samame gidan Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na APC."
"Kuma ya yi ikirarin jami'an sun gano maƙudan kuɗi biliyan N400bn. Muna sanar da cewa ko kaɗan EFCC ba ta kai wannan samame ba, don haka muna kira ga ɗaukacin al'umma su yi fatali da labarin su ɗauke shi ƙanzon kurege."
A wani labarin kuma An gano Yadda Wasu Mutum 2 a Aso Rock Suka Sauyawa Buhari Tunani Kan N500 da N1000
Wasu majiyoyi masu karfi sin bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga damuwa bayan samun labarin talakawa sun shiga wahala sanadin sauya naira.
Sai dai majiyar ta ce Buhari na gab da ɗaukar zaɓi ɗaya daga cikin abu uku don saukakawa yan kasa, sai wasu mutum 2 suka hure masa kunne.
Asali: Legit.ng