Yadda Wasu Mutum 2 a Aso Rock Suka Sauyawa Buhari Tunani Kan N500 da N1000

Yadda Wasu Mutum 2 a Aso Rock Suka Sauyawa Buhari Tunani Kan N500 da N1000

  • Ga dukkan alamu kalaman gwamnan Kaduna kan mutanen fadar shugaban kasa akwai ƙamshin gaskiya
  • Wasu bayanai sun fallasa yadda wasu mutane biyu a Villa da suka sauya wa shugaban kasa tunani kan tsawaita wa'adi
  • Har yanzun dai batun na gaban Kotun koli amma Buhari ya yi kunnen uwar shegu da umarnin Kotu

Abuja - Wasu bayanan gaskiya da suka fito jiya sun nuna cewa wani Minista da babban jami'in gwamnati a Villa ne suka sauya aniyar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na ƙara wa'adin amfani da tsoffin naira.

The Nation ta ruwaito cewa bayanan sun nuna cewa manyan kusoshin biyu ne suka sauya wa Buhari shirinsa na sanar da ƙara wa'adin tsoffin N200, N500 da N1000 zuwa 10 ga watan Afrilu.

Haka zalika an ce gwamnoni sun amince da tsawaita wa'adin duk da cewa sun nemi a ƙara akalla wa'adin shekara ɗaya na sauya tsoffin naira da sabbi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

Shugaba Buhari.
Yadda Wasu Mutum 2 a Aso Rock Suka Sauyawa Buhari Tunani Kan N500 da N1000 Hoto: CBN
Asali: Facebook

Yayin tattaunawa da jami'an FG, gwamnoni sun yi ikirarin cewa bincike ya nuna sashin buga kuɗi zai kwashe mafi ƙaranci watanni Tara kafin ya buga sabbin naira Tiriliyan ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan binciken jaridar ya gano cewa kafin jawabin kai tsaye, shugaban kasa ya samu rahoton tsaro kan halin da aka shiga a ƙasar nan sakamakon sabon tsarin CBN.

Baya ga wannan rahoton, Buhari ya samu labarin cewa tsarin ya jefa talakawa cikin ƙarin matsin rayuwa. Wata majiya tace ya lissafo zaɓuka uku da zai nemi shawari gabanin yin jawabi ga 'yan ƙasa.

Abubuwa ukun da Buhari ya ɗauka

Zabin da shugaban kasa ya ayyana sune;

1. Sake nazari da kuma duba yuwuwar soke sabon tsarin sauya fasalin naira.

2. Sake barin tsoffin N200, N500 da N1000 su ci gaba da yawo hannun jama'a har zuwa 10 ga watan Afrilu, 2023.

Kara karanta wannan

"Ka Bani Mamaki" Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga Jawabin Shugaba Buhari Kan Karancin Naira

3. Barin Kotu ta yanke hukuncin karshe kan sauya fasalin kiɗin.

An yi kokarin sulhu a cikin gida don ceto tattalin arziki

Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa:

"Bayan killace waɗan nan hanyoyin, shugaban kasa ya fara tattaunawa da gwamnoni, makusanta, masana dabaru da kuma auna tunanin gwamnan CBN, Godwin Emefiele."
"Shugaban kasa ya nuna tsantsar damuwa da jin talakawa ne ƙarancin naira ya yi wa babbar illa, duba da tabbacin da Emefiele ya gabatar masa, ya yi fatan tsarin zai gudana cikin sauƙi."
"Buhari ya ɗauki dalilan masu cewa ya sake nazari, abinda ya fi damunsa yadda talakawan da suka sha gumi suka samu kuɗinsu suke wahala wajen neman sabon naira da zasu ciyar da iyalansu."

Majiya ta ƙara da cewa shugaba Buhari ya yanke shawarin barin tsoho da sabbin kuɗin su ci gaba da yawo hannun jama'a har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu amma wasu suka canja masa tunani.

Kara karanta wannan

Karin bayani: El-Rufai ya tona asirin Buhari da CBN kan batun tsawaita wa'adin tsoffin Naira

Wani Minista da na kusa da shugaban kasa ne suka sa Buhari ya sauya tunaninsa, ya yi jawabi kai tsaye ranar Alhamis da ta gabata.

Majiyar ta ci gaba da cewa:

"Mutanen biyu sun gamsar da Buhari cewa ƙara wa'adin N500 da N1000 zuwa 10 ga watan Afrilu, zai kawo karshen yunƙurinsa na hana yan siyasan da suka maƙare biliyoyin nairori da nufin sayen kuri'u."
"Sun gamsar da shugaban kasan cewa yan Najeriya zasu fahimce shi idan ya musu jawabi kai tsaye, zasu amince kuma su rungumi sabon tsarin."

Su waye waɗannan mutum biyun?

Da majiyar ke amsa tambayar ko su waye mutanen, ta ce:

"Jami'an biyu mambobin majalisar zartaswa ne dake kokarin yaƙar ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu saboda burinsu bai cika ba."
"Ɗaya daga cikinsu ya nemi zama gwamna yayin da ɗayan kuma ya so a ba shi takarar mataimakin shugaban kasa. Buhari ya yi tunanin suna da hujja ba tare da sanin manufarsu ba."

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Bayan Zaman Kotun Koli, Shugaba Buhari Ya Sake Kus-Kus da Emefiele, Bayanai Sun Fito

A wani labarin kuma Matakai Uku Da Zaku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

Idan baku mata ba gwamnan CBN ya tabbatar da cewa wa'adin tsohon naira ya cika tun 10 ga watan Fabrairu, 2023 kuma shugaban ƙasa ya tabbatar.

Sai dai duk da haka akwai wasu matakai da yan Najeriya zasu bi wajen mayar da tsoffin N500 da N1000 ga bankuna cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel