Ganduje ya yi wa Buhari Gori, ya yi Masa Mummunar Watsa-Watsa a kan Canjin Kudi

Ganduje ya yi wa Buhari Gori, ya yi Masa Mummunar Watsa-Watsa a kan Canjin Kudi

  • Abdullahi Umar Ganduje ya yi wasu kalamai masu zafi da ake ganin da Muhammadu Buhari yake
  • Gwamnan na Jihar Kano ya yi tir da canjin kudi da aka yi, yana zargin an yi shi ne domin a rusa farar hula
  • Dr. Ganduje ya soki Gwamnan CBN, yana mai alwashin fatattakar tsare-tsarensa idan har suka lashe zabe

Kano - A wani sauti da aka fitar a gidan rediyon Express Radio Nigeria, an ji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana sukar tsarin canza kudi da aka kawo.

Daga bayanin Abdullahi Umar Ganduje, za a iya fahimtar cewa yana zargin Mai girma Shugaban kasa da yunkurin tarwatsa jam’iyyar da ta ba sa damar mulki.

Dr. Abdullahi Ganduje ya tunawa Muhammadu Buhari yadda ya yi ta takara ba tare da samun nasara ba, kafin su yi wa PDP taron dangi a Jam’iyyar APC a 2015.

Kara karanta wannan

Rana Mai Tarihi: Sanusi Ya Shiga Kano a Karon Farko Tun Tsige Shi Daga Sarauta

A cewar Gwamnan na APC, tsarin mulkin farar hula ya lalace a karkashin mulkin gwamnatinsu.

Habu na Habu?

“Babu shakka mun san darajar ‘dan siyasa, shiyasa yanzu idan ka duba abubuwan da su ke faruwa, sai ka ji kamar ka yi kuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ka dubi mutum ya yi takara, ya yi takara bai ci ba, aka zo aka yi hadin-gwiwa ya ci zabe, ya yi shekara hudu, ya sake cin zabe.
Yanzu zai fita, babu abin da ake yi illa jam’iyyar da ta zabe shi, ya lalata ta..."

- Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje
Shugaba Buhari da Ganduje a 2019 Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Ganduje ya cigaba da jawabi

"...Yanzu saboda Allah mutum ya zama Habu na Habu? Kai ka tara kayanka, kuma kai ka watsa kayanka!
Lokacin zabe ya zo, an auna a kawo wannan doka? Saboda Allah wannan doka, menene ma’anarta? Menene idan an yi ta bayan zabe? Kuma menene ya sa ba ayi ta shekara bakwai da rabi?"

Kara karanta wannan

Alkawari kaya ne: Tinubu ya fadi abu 1 da zai yiwa ASUU kowa ma ya huta idan ya gaji Buhari

- Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya caccaki Gwamnan CBN

Daily Trust ta ce Gwamnan ya yi tir da Godwin Emefiele, ya ce bankin Duniya da asusun IMF duk sun soki tsarin canza manyan takardun Nairori.

“Duk ‘dan siyasa sai ya ji menene amfani wannan Gwamnan babban banki (Godwin Emefiele).
Yanzu mutum yana shugaba, yana ganin banki yana cin wuta, idan ba don damukaradiyya ta lalace ba, haka ta yiwu?
Wannan ba shi da amsa kwata-kwata. Kuma damukaradiyya ba ta gaji wannan ba.”

- Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin rikon kwarya

A jawabin, an ji Abdullahi Ganduje ya ce sun shigar da karar gwamnatin tarayya, su na zargin ana kokarin kafa irin gwamnatin rikon kwaryar da aka yi a 1993.

A cewarsa, lamarin ya fi karfin a ce ana hana wani cin zabe, Gwamnan ya sha alwashin ruguza wadannan tsare-tsare da aka fito da su da zarar APC tayi nasara.

Kara karanta wannan

Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

Asali: Legit.ng

Online view pixel