Gwamnan APC Ya Yiwa Emefiele Wankin Babban Bargo Kan Sauya Fasalin Kuɗi

Gwamnan APC Ya Yiwa Emefiele Wankin Babban Bargo Kan Sauya Fasalin Kuɗi

  • Gwamnan jihar Ondo ya koka kan illar da tsarin sauya fasalin kuɗi ke yiwa jam'iyyar su ta APC
  • Gwamnan yayi nuni da cewa tsarin ba a fito da shi lokacin da ya dace ba saboda haka dole a jingine shi gefe guda
  • Akeredolu ya kuma bayyana dalilin da ya sanya Emefiele ya turje lallai sai aiwatar da tsarin

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bayyana cewa tauraruwar jam'iyyar APC na ƙara dusashewa saboda wahalar da ƴan Najeriya ke sha kan sauya fasalin kuɗi.

Jihar Ondo na ɗaya daga cikin jihohin da suka maka babban bankin Najeriya (CBN) ƙara a kotun ƙoli kan shirin sauya fasalin kuɗi na bankin.

Da yake magana akan tsarin na sauya fasalin kuɗin a ranar Laraba, Akeredolu yace ba ayi tsarin lokacin da yakamata ba saboda haka dole a sauya shi. Rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Akeredolu
Gwamnan APC Ya Yiwa Emefiele Wankin Babban Bargo Kan Sauya Fasalin Kuɗi
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Muna da matsala da muke fuskanta a ƙasar nan. Farin jinin jam'iyyar mu yayi ƙasa. Kada mu yaudari kan mu. Dole sai a wannan lokacin za a samar da wannan sabon tsarin na tattalin arziƙi?
“Ta yaya? Man fetur da komai? Abubuwa sun yi tsauri. Wannan tsarin bai dace ba a wannan lokacin. Dole a sauya shi. A ajiye shi gefe guda sannan a gayawa CBN an dakatar da shi. A cigaba da amfani da sabbi da tsofaffin kuɗi tare."
"Ƴan achaɓa, masu tasi, bankuna sun daina karɓar tsofaffin kuɗi. Akwai umurnin kotu amma kowa yana yadda yaga dama kamar ba wannan umurnin. Mun faɗa cewa yakamata a kori Emefiele tun lokacin da ya nemi yin takarar shugaban ƙasa."
Kwata-kwata Emefiele bai cancanci riƙe wannan muƙamin ba. Mutumin da yayi ƙoƙarin zama shugaban ƙasa dole ya ɓata mana rai a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamna Wike Ya Kara Magana Kan Sauya Naira, Ya Tona Asirin Masu Goyon Bayan CBN

A watan Mayun 2022, Akeredolu ya nemi Emefiele da yayi murabus daga muƙamim sa idan har yana son ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Shugaban Majalisa Ya Fallasa Masu Hannu Dumu-Dumu a Canjin Kudi da Wahalar Fetur

A wani labarin na daban kuma, Femi Gbajabiamila, ya fasa ƙwai inda ya bayyana masu hannu kan sauya fasalin kuɗi.

Shugaban majalisar yayi zargin cewa an kawo tsarin sauya fasalin kuɗin ne domin a yiwa ɗan takarar su na APC, Bola Tinubu, illa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel