2023: Bola Tinubu, Shettima Sun Gana da Gwamna Wike a Patakwal

2023: Bola Tinubu, Shettima Sun Gana da Gwamna Wike a Patakwal

  • Mai neman zama shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, abokin gaminsa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni sun gana da Wike
  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, na cikin tawagar Tinubu amma ba'a ga ƙeyar tsohon ministan Sufuri ba
  • Kwamitin kamfen shugaban kasa na APC ya gudanar da rali a jihar Ribas ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu

Rivers - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, da abokin gaminsa, Sanata Kashim Shettima, sun ziyarci gwamnan Ribas, Nyesom Wike a gidan gwamnati dake Patakwal.

Channels tv ta ruwaito cewa Tinubu da Shettima sun ziyarci Wike tare da rakiyar shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, 2023.

Gwamna Wike da Tinubu.
2023: Bola Tinubu, Shettima Sun Gana da Gwamna Wike a Patakwal Hoto: vanguard
Asali: UGC

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, gwamna Dave Umahi na Ebonyi, da Babjide Sanwo-Olu na Legas na cikin tawagar Bola Tinubu da ta gana da Wike a gidan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Buhari Ya Zaba Ya Darje Tsakanin Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Wanda Zai Share Hawayen Yan Najeriya

Vanguard tace sauran jiga-jigan da suka halarci ganawar sun haɗa da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, bai je wurin ganawa da Wike ba kamar yadda aka yi tsammani.

Haka zalika, ɗan takarar gwamnan Ribas a inuwar APC, Mista Tonye Cole, ya bi sahun Amaechi, bai halarci taron ba.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa sai da Tinubu ya gama yakin neman zaɓen APC daga bisani ya zarce zuwa wurin Wike a gidan gwamnatin Ribas.

Gwamna Wike, jagoran tawagar gaskiya ko G-5 ya samu saɓani da ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa PDP, Atiku Abubakar, tun bayan gama zaɓen fidda gwani.

APC ta ƙara karfi a jihar Kebbi

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi da Zamu Saka Wa Tinubu Alherin Da Ya Mana, Gamayyar Yan Arewa

A wani labarin kuma Jam'iyyar SDP Ta Rushe Tsarinta, Ta Koma Inuwar APC Mai Mulki a Kebbi

Social Democratic Party (SDP) ta rsuhe baki ɗaya tsarinta yayin da ɗan takarar gwamna da shugabanni suka tattara suka koma APC.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ciyaman na ƙungiyar gwamnonin APC ya ce yan siyasna sun ɗauki matakin da ya dace da suka shiga inuwar APC ana shirin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel