Rabiu Kwankwaso ya Ziyarci Jihar Arewa Sau 2 a Kwana 15 Domin Samun Kuri’u a NNPP

Rabiu Kwankwaso ya Ziyarci Jihar Arewa Sau 2 a Kwana 15 Domin Samun Kuri’u a NNPP

  • A karo na biyu a cikin kusan makonni biyu, Rabiu Musa Kwankwaso ya sake sa kafafunsa a Neja
  • Kwanakin baya ‘dan takaran na NNPP ya ziyarci New Bussa, a makon nan ya je garin Kontagora
  • Rabiu Kwankwaso ya ba jihar Neja muhimmanci, ya yi kira ga jama’a da su zabi jam’iyyar NNPP

Niger - Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci garin Kontagora a jihar Neja domin ya cigaba da tallata jam’iyyarsa ta NNPP da yake neman mulkin kasa.

Legit.ng Hausa ta samu labari Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya isa Kontagora a jirgi mai saukar ungulu da kimanin karfe 3:300 na yammacin Litinin.

Kamar yadda ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar NNPP ya bayyana, ya kai wa sabon Sarki, Mai martaba Alhaji Muhammad Barau ziyara a fadarsa.

Sarki Muhammad Barau ya karbi ‘dan takaran da hannu biyu-biyu, kuma ya yi masa addu’a.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

Kontagora ta karbi Kwankwaso

Daily Trust a rahoton da ta fitar, ta ce dinbin mutane suka tarbi Kwankwaso da tawagarsa a yayin da ya yi kira a gare su da su zabi jam’iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Gwamnan na Kano ya godewa mutanen jihar Neja, musamman Kontagorawa ganin yadda mutane su ka fito nuna masu goyon baya a zaben 2023.

Rabiu Kwankwaso
Tawagar Kwankwaso a garin Kontagora Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A zabi 'yan takaran NNPP - Kwankwaso

Kwankwaso ya tallata jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, ya ce ta tsaidawa mutanen jihar Neja ‘yan takara na kwarai masu kaunar talakawa.

Mun ji Sanata Kwankwaso yana cewa tsarin Kwankwasiyya tafiyar talakawa ce wanda ba su yi imani da aiki da kudi domin sayen jama'a da zabe ba.

A jawabin da ya yi, ‘dan takaran shugaban kasar ya roki Ubangiji ya karkato hankalin talakawan Neja da na Najeriya su zabi ‘yan siyasa masu son jama’a.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Zai Iya Jawo Barkewar Rigima a Sakamakon Zaben 2023

An soki tsarin canza kudi

Har ila yau, tsohon Ministan tsaron ya soki tsarin canjin kudi da aka fito da shi, ya ce gwamnati tarayya tayi hakan ba tare da yin shawara da mutane ba.

Baya ga zargin mulkin APC da kashe kasa, ‘dan siyasar ya ce an raina talaka, masu mulki su na jin sun fi karfin kowa a yau duk da talaka ne ya zabe su.

Zuwa kimanin karfe 6:00, Kwankwaso da mutanensa su na filin tashi da saukar jirgin sama na Nnamdi Arzikwe da ke garin Abuja, ya koma gidansa.

Nyako za su taimakawa Tinubu

An rahoto cewa Sanata Abdulaziz H. Nyako ya ce da aka tsige ubansu daga kujerar Gwamna, Bola Tinubu ya yi masa rana, ya tsere zuwa birnin Landan.

'Dan takaran APC a yau, Asiwaju da Bukola Saraki suka taimakawa Admiral Murtala Nyako (rtd) ya bar kasar nan lokacin da ya yi fada da Gwamnatin PDP.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tsage Gaskiya, Ya Faɗi Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Iya Cin Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng