Ba'a Taba Gwamnan CBN Mai Kawo Rudani Irin Emefiele Ba, Tsohon Minista

Ba'a Taba Gwamnan CBN Mai Kawo Rudani Irin Emefiele Ba, Tsohon Minista

  • Shugaban SWAGA, Dayo Adeyeye, ya soki gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, kan sabon tsarin sauya naira
  • Tsohon karamin ministan ayyukan ya ce Emefiele ya kafa tarihin gwamnan CBN mafi ruɗani da rashin tabbas a Najeriya
  • Mista Adeyeye ya yaba wa yan Najeriya bisa fahimtar halin da ake ciki kuma ya ce Tinubu ne da nasara a zaben 2023

Akure, Ondo - Dayo Adeyeye, shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu a kudu maso yamma (SWAGA) ya caccaki gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ranar Litinin.

Mista Adeyeye ya bayyana Emefiele da, "Mafi ruɗanin gwamnan CBN," da aka taɓa gani a tarihin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sauya takardun naira.
Ba'a Taba Gwamnan CBN Mai Kawo Rudani Irin Emefiele Ba, Tsohon Minista Hoto: CBN
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne yayin da ake tsaka da ƙarancin sabbin takardun naira da kuma matakin wasu bankunan kasuwanci na daina karban tsohon kuɗi a wasu sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: CBN Ya Zo Da Sabon Shiri Mai Kyau Na Kawo Karshen Karancin Sabbin Kuɗi a Najeriya

Da yake jawabi a Akure, jihar Ondo ranar Litinin, Dayo Adeyeye, tsohon ƙaramin ministan ayyuka ya yi zargin cewa gwamnan CBN na da wata manufa daban ta rusa shirin babban zaɓe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar tsohon minista, sabon tsarin babban banki CBN na sauya fasalin N200, N500 da N1000 ya hukunta da yawan yan Najeriya da ƙunci da wahalar rayuwa.

A ruwayar Tribune, Adeyeye ya ce:

"Hukunci mara daɗi da CBN ya kakaba wa yan Najeriya bai zama dole ba, Emefiele da yan kanzaginsa na da wani buri a zuci. Da wannan abu, sun kuntatawa yan Najeriya, ya kamata Emefiele ya dau shawarin Tinubu."
"Godwin Emefiele ya zama gwamnan CBN mafi kawo ruɗani da gardama a tarin Najeriya. Ko yana so ko baya so 'yan Najeriya sun gano duk abinda ke wakana kuma Tinubu zai samu nasara."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Kwana 13 Gabanin Zabe, An Nemi Kuɗin Kamfen Atiku An Rasa, Jigon PDP Ya Tona Masu Hannu

"Muna jinjinawa talakawan Najeriya musamman 'yan kasuwa mata, waɗanda suka fahimci batun yadda ya kamata."

Shin CBN Ya Kara Wa'adin Amfani da Tsoffin Kuɗi? Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani

A wani labarin kuma Mun tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da yaushe ne wa'adin CBN bayan 10 ga wata ta wuce

Tuni dai wasu yan kasuwa suka fara kin karban tsohon takardan naira saboda rashin sanin takamaiman ranar haramta tsaffin kudin a hukumance.

Kotun Ƙoli ta umarci gwamnatin tarayyya ta jinkirta aiwatar da sabon tsarin har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu da zata ci gaba da shari'a kan batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel