Magajin Buhari: Atiku Ya Bugi Kirji Cewa Shine Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa
- Yan kwanaki kafin babban zaben Najeriya, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya yi hasashen yadda zaben za ta kasance
- Atiku wanda ya karfafawa mabiyansa gwiwa, ya bugi kirjin cewa ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ya gama
- Iyorchia Ayu ya yi kira ga al'ummar kudu maso gabas da kada su zabi Peter Obi don ba zai kai labari ba
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bugi kirji cewa jam'iyyarsa ce za ta lashe zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Da yake jawabi ga magoya baya da jiga-jigan jam'iyyar a Umuahia, babban birnin jihar Abia, a ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairu, Atiku ya bukaci magoya bayansa da kada su bari sauran jam'iyyun siyasa su dauke masu hankali domin sune za su lashe zaben.
Kada ku zabi Peter Obi a zabe mai zuwa, Ayu ga mutanen kudu maso gabas
A jawabinsa, shugaban PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya yi kira ga mutanen yankin kudu maso gabas da kada su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce zabar Obi zai kara karfafa damar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ke da shi ne kawai.
Ya ce:
"PDP za ta lashe zaben. Don haka, zai fi dacewa ku kasance a tikitin nasara maimakon a tikitin da ba zai kai ku ko'ina ba.
"Ina rokonku da kada ku yarda sauran jam'iyyun siyasa da ke buga wasarsu da addini ko kabilanci su janye maku hankali. A PDP, ba mu da katin addini ko kabilanci, katin Najeriya kawai muke kadawa.
"Katin za zai tafi da kowa, katin da zai baku darajarku a kowani yankiu na kasar nan, ga kowani addini, ga kowani kabila."
Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamnan Abia, Dr. Okezie Ikpeazu, bai halarci gangamin kamfen din na Atiku ba a jiya Asabar.
Za a yi maka taron dangi a Arewa, Primate Ayodele ga Peter Obi
A wani labarin, babban malamin addinin Kirista a Najeriya, Primate Ayodele, ya ja hankalin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, gabannin zaben 2023.
Primate Ayodele ya ce za a yi wa Obi taron dangi a arewa saboda kada ya kai labari a zaben mai zuwa, sai dai kuma ya ce Allah ya nuna masa cewar ba za a yi juyin mulki ba kasar don bai yarda da shi ba.
Asali: Legit.ng