Zaben 2023: Hedkwatar Tsaro Ta Yi Watsi Da Ikirarin Cewa Atiku Na Aiki Da Sojoji Don Yin Juyin Mulki

Zaben 2023: Hedkwatar Tsaro Ta Yi Watsi Da Ikirarin Cewa Atiku Na Aiki Da Sojoji Don Yin Juyin Mulki

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa Atiku Abubakar na aiki da sojoji don tarwatsa zaben 2023
  • Da take martani ga ikirarin a ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairu, Hedkwatar Tsaro ta bayyana cewa aikin wasu marasa gaskiya ne
  • DHQ ta kuma ce za a gayyaci masu yada wannan labari nan ba da jimawa ba don tabbatar da ikirarinsu

Abuja - Hedkwatar tsaro (DHQ) ta yi martani ga zargin cewa wasu jami'an sojoji masu ci na aiki tare da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) don hargitsa babban zabe mai zuwa.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairu, Birgediya Janar Tukur Gusua, mukaddashin daraktan labarai na tsaro, ya karyata ikirarin.

Atiku da sojoji
Zaben 2023: Hedkwatar Tsaro Ta Yi Watsi Da Ikirarin Cewa Atiku Na Aiki Da Sojoji Don Yin Juyin Mulki Hoto: @atiku, @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Gusau ya bayyana ikirarin a matsayin mummunan farfaganda daga wasu mutane marasa gaskiya.

Kara karanta wannan

Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

Ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya bata ji dadi ba cewa mutanen da ake sa ran za su zama wayayyu a siyasance za su iya kaskantar da kansu sannan su fito da irin wannan ikirari, rahoton The Cable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za mu gayyaci masu farfagandan don tabbatar da ikirarinsu, DHQ

Hedkwatar tsaron ta fito fili ta bayyana cewa tana mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya kuma cewa ba za ta taba kasancewa da hannu wajen shirya kowani makirci don kaskantawa ko murkushe damokradiyyar kasar ba.

Don haka, ta yi gargadin cewa za a gayyaci wadanda ke yada irin wannan zarge-zargen nan ba da jimawa ta don tabbatar da ikirarinsu.

PR Nigeria ta nakalto wani bangare na sanarwar na cewa:

"Rundunar sojojin Najeriya ta ji takaici cewa hatta ga mutanen da suke da wayewa a bangaren siyasa za su iya kaskantar da kansu wajen hada kai da masu kokarin kawo hargitsi da rikici wajen yin ikirarin karsa don haifar da tashin hankali a siyasa.

Kara karanta wannan

Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

"Ya zama dole a bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya runduna ce kwararriya da ke biyayya ga kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya kuma ba za a taba hada kai da ita don shirya mugun nufi a kan damokradiyyarmu ba.
"Baya ga haka, rundunar soji bata siyasa kuma tana tsaka-tsaki a tsarin siyasar da ke gudana a yanzu kuma ba za ta taba saka kanta a wannan zargi da ake mata ba.
"Rundunar sojojin Najeriya ba za ta taba kasancewa a cikin kowani makirci don tarwatsa damokradiyyar da aka sha wahala wajen samunta ba."

Shugaban yakin neman zaben Atiku ya yi wa Tinubu kyakkyawar tarba a Sokoto

A wani labarin, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto kuma darakta janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC kyakkyawar tarba da ya je jiharsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel