Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

  • Mai bada shawara kan tsaron kasa ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin sauya fasalin Naira
  • Majalisar wakilan tarayya na cigaba da yunkurin ganin cewa an soke shirin hana amfani da tsaffin kudi
  • Majalisar magabata da masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa a cigaba da amfani da sabbin kudi amma a tabbata sun wadatu

Dokar canja fasalin kuɗi da Amfani dasu ta babban bankin Najeriya CBN zai kawo wa Sojoji tasgaro a ayyukan su.

Hakan ya fito daga bakin mai bawa shugaban ƙasa shawara akan harkokin tsaro NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai ritaya), yayin da ya bayyana a gaban wani kwamiti na majalisar wakilan tarayyar ranar Alhamis, rahoton Punch.

Monguno ya furta hakan ne ta bakin wakilin sa Adimiral Abubakar Mustapha.

Ya ce saboda tasiri da muhimmancin wasu bayanai na tsaro, ai masa afuwa bazai samu damar furta su a gaban manema labarai ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Da Sharadi 1: Majalisar Magabata

Kai tsaye shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ta ƙasa, Alhassan Ado-Doguwa, ya umarci ƴan jarida da masu taimaka su bar daƙin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Repss
Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno
Asali: UGC

Mustapha ya ce shine mai bada umarni dake da alhakin kula da sakatariyar ta ofishin mai bawa ƙasa shawara akan harkar tsaro wacce ke kula da auna yanayin tsaron da yake a lokacin zaɓuɓɓuka da sauran wuraren dake fama da sa-toka-sa-katsi na tsaro gamida kula da yanayin kota-kwana da ujilar tsaro da ofishin ke samarwa.

Bugu da ƙari, ya kuma bawa kwamatin haƙuri:

“A madadin mai gidana, wanda bai samu halartar wurin nan mai muhimmanci ba saboda wani ƙwaƙwƙwaran uzuri da yasha kansa “.

Ya ce Mongunu yana wajen Najeriya domin halartar wani zaman tattaunawa mai matuƙar muhimmanci wanda saboda haka ne aka umarce shi domin ya wakilci mai bawa ƙasar shawara akan harkar tsaro.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Bankuna Sun Haɗe Kai, Sun Fitar da Sabuwar Sanarwa Ana Tsaka da Rashin Sabbin Kuɗi

Mustapha ya ƙara da cewa,

“Ba zan gushe ba, sai na ƙara da cewa, idan akai duba da tarayya ta duniya, za’a ga cewa, dokokin taƙaita zirga-zirgar kuɗi a hannun mutane da ire iren su da ake sakawa ba tare da an tauna an furzar ba, suna da matuƙar tasiri ga gudanar da harkokin gudanarwa ta sojoji, koda a ƙasashen da suka ci gaba ne."
"Saboda haka, idan ba’a auna ba aka sanya su, dole zasuyi wa harkokin sojoji illa, musamman ga gwarazan sojojin mu da aka tura wuraren da bazasu samu damar mallakar na’urorin da zasu biya ko amshi ƙudi ta manhajar kan waya ba."
"Hakan ka iya hana su biyan kuɗin kayan masarufi. Wannan shine babban maudu’in da mai bawa tsaron ƙasa akan harkar tsaro yake ta jan hankali akai.”

Alhassan Ado-Doguwa a nasa bangaren yace:

“Duba da abin da yake faruwa, ma’aikatar kuɗi ta tarayya na da muhimmiyar rawa da zata taka a cikin wannan balahirar, saboda haka muna umartar ma’aikatar kuɗin ta ƙasa dasu bayyana a gaban wannan kwamati mai muhimmanci. Idan suka ƙi zuwa kuwa, tabbas zamu yi amfani da ƙarfin da doka ta bamu domin tanƙwara su zuwa gaban wannan kwamati.”

Kara karanta wannan

Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

Tun da fari, Ado Doguwa furta cewa Kwamitin yana aiki tuƙuru ne a wani salon ƙoƙarin ganin sun binciki yadda dokar rage zirga-zirgar kuɗi a hannun mutane ta babban bankin Najeriya ke tasiri akan tattalin arzikin ƙasa da babban zaɓen ƙasa da za’a gudanar na 2023 da yake tunkarar kasa.

Majalisar ta naɗa kwamitin ne na wucin gadi akan dokar babban bankin Najeriya na taƙaita zirga-zirgar kuɗi tsaba a hannun jama’a domin ƙara wa’adin musanya tsofaffin kuɗaɗe da sababbi.

Ya ƙarƙare da cewa:

“ Yana da kyau a sani cewa, wannan abu da muke munayi ne domin ci gaba da gudanar da aikin da doka bamu dama a matsayin mu na kwamitin wucin gadi na majalisar dokoki ta tarayya akan dokar canja fasalin kuɗi da kuma canjin kuɗi na tarayyar Najeriya.” Inji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel