An Raunata Mutane 15 Yayin da Yan Daba Suka Kai Hari Gidan Dan Majalisa

An Raunata Mutane 15 Yayin da Yan Daba Suka Kai Hari Gidan Dan Majalisa

  • Yan daban siyasa sun kai hari gidan ɗan majalisar tarayya a jihar Osun, sun jikkata magoya bayansa 15 ranar Jumu'a
  • Wole Oke, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Obokun/Oriade, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa
  • Rundunar yan sanda tace ta kama ɗaya daga cikin yan daban kuma ya fara bayani kan waɗanda suka turo su

Osun - Rahotanni sun nuna cewa mutane 15 suka ji raunuka ranar Jumu'a lokacin da wasu 'yan daban siyasa suka kai hari gidan ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Obokun/Oriade a Osun, Wole Oke.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa gidan mamban majalisar na cikin rukunin gidajen gwamnatin da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Wole Oke.
An Raunata Mutane 15 Yayin da Yan Daba Suka Kai Hari Gidan Dan Majalisa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun zo ɗauke da bindigu, Adduna, fasassun kwalabe, da sauran muggan makamai.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Daba Sun Kaiwa Magoya Bayan Peter Obi Hari a Legas, Sun Tafka Ta'adi

Mista Oke, a wata sanarwa da ya fitar jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce mutane 15 da aka jikkata suna cikin magoya bayansa da suka kai masa ziyara har gida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Wasu Hausawa daga karamar hukumar Obokun, sun zo gidana dake GRA su jaddada goyon bayansu gare ni a Osogbo ranar Jumu'a ba zato suka kawo hari."
"'Yan daban da ake zaton na siyasa ne sun ji masu raunukan yanka, duka da sanduna da sauran makamai masu haɗari. Kusan mutum 15 daga ciki sun ji raunka."
"Nan take aka garzaya da su Asibiti domin kula da lafiyarsu. Ɗaya daga cikin maharan ya shiga hannu, ya bayyana cewa wani ɗan siyasan Osogbo ne ya turo su."

Muna kan bincike - Yan sanda

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ɗaya daga cikin maharan ya shiga hannu, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

"Hukumar yan sanda ta samu masaniya kuma an damƙe ɗaya daga cikin maharan, a halin yanzu muna kan bincike," inji shi.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Mista Oke, mamban majalisar wakilan tarayya a karo na hudu, mamba ne a jam'iyyar PDP.

A wani labarin kuma Mambobin APC a Jihar Ebonyi Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP

Mako biyu gabanin babban zaben 2023, jam'iyyar PDP ta ƙara karfi a jihar Ebonyi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu daruruwan mambobin jam'iyyar APC mai mulki sun tabbatar da sauya sheka zuwa PDP ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel