Darakta Janar Na Kamfen Atiku a Jihar Ribas Ya Tsallake Rijiya da Baya
- Wasu muyagun 'yan bindiga sanye da kayan 'yan sanda sun kai wa Daraktan Kamfen Atiku Abubakar na jihar Ribas hari ranar Alhamis
- Bayanai sun nuna cewa Dakta Abiye Sekibo, ya je duba wurin da suke shirin tarban tawagar kamfen Atiku lokacin da lamarin ya faru
- Da yake zantawa da 'yan jarida a Patakwal yau Jumu'a, DG ya ce maharan sun yi kaca-kaca da motarsa kuma sun cinna wuta a wurin ralin
Rivers - Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a inuwar PDP reshen jihar Ribas, Dakta Abiye Sekibo, ya shallake rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka farmake shi ranar Alhamis.
Rahoton Daily Trust ya ce 'yan bindigan sanye da Kakin 'yan sanda sun buɗe wa Motar sulken Dakta Sekibo wuta a garin Rainbow da ke Patakwal, babban birnin jihar.
An tattaro cewa Sekibo ya je duba wurin da za'a gudanar da gangamin kamfen shugaban kasa na PDP lokacin da maharan suka farmake shi ba zato ba tsammani.
Da yake hira da manema labarai kan lamarin a Patakwal ranar Jumu'a 10 ga watan Fabrairu, 2023, Dakta Sekibo, ya ce motarsa ta yi kaca-kaca a harsashi haka nan kuma mahran sun cinna wuta a wurin Ralin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa ya ce:
"Yayin da muka tunkari wurin, wasu 'yan sanda waɗanda ke kallon yadda wutar ke ci suka buɗe wa Motar da muke ciki wuta."
"Dana ɗaga kai na kalli Motar Hilux ɗin da suke zo da ita, na gane motar 'yan sanda ce da ke cikin ayarin gwamnan jihar Ribas (Nyesom Wike)."
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa har zuwa yanzun rundunar 'yan sanda reshen jihar Ribas ba ta fitar da sanarwa kan sabon harin ba.
Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas Ya Tsallake Harin Kisan da Aka Kai Masa
A wani labarin na daban kuma 'yan bindigan da ba'a sani ba sun kaiwa ayarin ɗan takarar gwamnan jihar Ribas hari
Rahoto ya ce Sanata Magnus Ngei Abe, mai neman zama gwamnan Ribas a iniwar SDP ya shallake rijiya da baya yayin da maharan suke bude wa tawagarsa wuta a Akinima.
An ce tun da farko tawagar ɗan siyasan sun ziyarci wasu kauyuka a yankin ƙaramar hukumar Ahoada ta yamma kafin su zarce Akinima inda lamarin da auku.
Asali: Legit.ng