Atiku Ya Bayyana Muhimmin Abinda Zai yi wa Jiha a Arewa Idan Ya Ci Zaben 2023

Atiku Ya Bayyana Muhimmin Abinda Zai yi wa Jiha a Arewa Idan Ya Ci Zaben 2023

  • 'Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha alwashin dawo da zaman lafiya a Yobe idan aka zabe shi
  • Bai tsaya nan ba, yace zai bude iyakokin Yobe da Nijar domin asassa kasuwancin tsakaninmu da makwabtanmu don inganta rayuwa
  • Yace zai tabbatar da da ya inganta rayuwar mata da matasa a fadin kasar nan idan har aka zabe shi a zaben watan nan da za a yi

Yobe - Atiku Abubakar, 'dan takarar kujerar shugabancin kasa na PDP, ya tabbatarwa da jama'ar jihar Yobe cewa zai dawo da zaman lafiya a jihar idan aka zabe shi.

Atiku yayi alkawarin sake bude iyokin Nijar da Yobe domin tabbatar da shige da ficen jama'a da kuma kayayyakin noma, Daily Trust ta rahoto.

kamfen din atiku
Atiku Ya Bayyana Muhimmin Abinda Zai yi wa Jiha a Arewa Idan Ya Ci Zaben 2023. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yayin jawabi a taron gangamin kamfen din PDP a jihar Yobe, Atiku yace idan aka zabe shi mulkinsa zai samar da kudin sana'o'i ga mata da matasa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Atiku yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan ku ka zabi PDP, zaman lafiya zai dawo Yobe. Za mu tabbatar da cewa an sake bude makarantun ku, ta yadda yaranmu za su cigaba da karatu.
"Mun kuma yi alkawarin tallafawa mata da matasa ta hanyar basu jari domin su kafa nasu kasuwancin don yi rayuwa mai cike da nasara.
"Mun yi alkawarin bude iyakoki ta yadda kasuwanci tsakaninku da makwabtanmu zai cigaba sosai."

Hakazalika, yayin jawabi, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, yace jama'a na cikin matsanancin hali saboda boye kudi don siyan kuri'a.

Ayu wanda ya tabbatar da cewa zaben na gaba yana gabatarwa da 'yan Najeriya dama ne na su farfado daga jam'iyyar mai mulki, ya tuna irin halin da 'yan Najeriya ke ciki sakamakon APC inda ya tabbatar da cewa Atiku zai farfado da su idan an zabe shi.

Kara karanta wannan

APC Ta Dage Kamfen Dinta Na Shugaban Kasa a Wata Jihar Kudu, Ta Fadi Dalili

Yace:

"Sun mayar da mu mayunwata, sun kawo rashin tsaro da sauran abubuwan da ba mu so. Ku zabi Atiku Abubakar, zai farfado da Najeriya.
"A batun musayar kudi, ba dukkansu bane suka amince. Ko wadanda suka amince din, boye kudin duke yi don siyan kuri;a, shiyasa mu ke wahala, kada ku yarda. Buhari yayi umarni ga jami'an tsari su kwato kudin da suke da shi."

Kotun koli ta ayyana Sanata Lawan 'dan takarar Yobe ta arewa a APC

A wani labari na daban, kotun koli ta ayyana Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, matsayin halastaccen 'dan takarar sanatan Yobe ta arewa.

Kotun tayi fatali da hukuncin kotun daukaka kara wacce ta bayyana Bashir Machina matsayin sahihin 'dan takarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel