Buhari Ya Fadawa Katsinawa Adadin Kuri’un da Yake so su ba Tinubu a zaben 2023

Buhari Ya Fadawa Katsinawa Adadin Kuri’un da Yake so su ba Tinubu a zaben 2023

  • Muhammadu Buhari ya nemi mutanen Katsina su ba Jam’iyyar APC kuri’u miliyan 2 a zaben 2023
  • Shugaban kasar ya fadawa Katsinawa su cigaba da zaben APC ko da zai bar mulki a watan Mayun nan
  • Bola Tinubu ya yi alkawari zai magance matsalar kashe-kashen da ‘yan bindiga suke yi a yankin Arewa

Katsina - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana sa ran jam’iyyar APC mai mulki za ta samu kuri’u miliyan daga jiharsa ta Katsina.

The Nation ta rahoto Mai girma shugaban Najeriyan yana cewa yana sa ran a zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a zaben 2023.

Muhammadu Buhari ya roki mutanen da suka je wajen taron da su fadawa abokai, ‘ya ‘ya da kuma ‘yanuwansu cewa su cigaba da zaben jam’iyyarsa.

An ji shugaban kasar yana cewa Bola Tinubu zai cigaba daga inda gwamnatinsa ta tsaya.

Kara karanta wannan

Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

"Ku fadawa abokanku, ‘yanuwanku maza da mata da ‘ya ‘yanku da su cigaba da zaben APC. Bola Tinubu zai cigaba daga inda muka tsaya.
Ku tabbata kuri’unku sun tafi wajen Tinubu a zaben shugaban kasa da Dikko Radda a zaben Gwamna da sauran ‘yan takaran jam’iyyar nan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Muhammadu Buhari

Buhari da Tinubu
Kamfen APC a Katsina Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Bola Ahmed Tinubu zai kawo tsaro

Premiuim Times ta ce a wajen taron yakin neman zaben da aka yi, ‘dan takaran kujerar shugaban kasa na APC, ya yi alkawarin yakar ‘yan bindiga.

Bola Tinubu yake cewa da gan-gan suka ki fasa dakatar da kamfe bayan kashe-kashen da aka yi saboda gudun a nunawa ‘yan bindiga an tsorata.

Kamar yadda Gwamna Aminu Bello Masari ya shaida a wajen taron, ‘dan takaran ya bada gudumuwar N100m ga wadanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Rahoton ya ce Shugaban kasa, Tinubu, Gwamna Atiku Bagudu da sauran ‘ya ‘yan APC sun yi wa Katsinawa ta’aziyyar ta’adin da aka yi masu kwanan nan.

Gwamnoni akalla bakwai, Ministoci, shugabannin jam’iyya da shugaban majalisa sun je taron.

Siyasar NNPP a Kano

Idan aka koma jihar Kano, za a ji labari Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce takarar Abba Kabir Yusuf a jam’iyyar NNPP ta samu gudumuwar N500m.

12.5% na gudumuwar da aka samu ta fito ne daga mazabar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayin da mutanen yankin Nasarawa suka bada N50m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel