Atiku Ya Je Kamfe, Gwamnan PDP da Duka Kwamishinoninsa Sun Yi Watsi da Shi
- Samuel Ortom da masu ba shi shawara ba su cikin wadanda halarci taron yakin neman zaben PDP
- Atiku Abubakar ya je kamfe a Benuwai amma Gwamna Ortom da Kwamishinoni ba su iya zuwa ba
- Shugaban jam’iyyar PDP ya roki Gwamnan Benuwai da mutanensa su hada-kai da Atiku a zaben 2023
Benue – Gwamna Samuel Ortom, mataimakinsa, Benson Abounu, ba su cikin wadanda suka halarci taron yakin zaben Atiku Abubakar a Makurdi.
Punch ta ce Mai girma Gwamnan da duka Kwamishanonin jihar Benuwai da Mukarabbansa da sun kauracewa taron da Atiku Abubakar ya yi a jiya.
Shugabannin kananan hukumomi 22 ba su je wajen gangamin jam’iyyar PDP ba. Irin haka ya faru kwanaki da Atiku suka hadu da su Ortom a filin jirgin sama.
PDP ta ke rike da jihar Benuwai, amma akwai sabani tsakanin Gwamnan jihar da Dr. Iyorchia Ayu wanda shi ne shugaban jam’iyyar na kasa baki daya.
Atiku yana tare da manyan PDP
Wadanda suka jagoranci taron yakin neman zaben Atiku Abubakar sun hada da tsohon Gwamna Sanata Gabriel Suswam da kuma Sanata David Mark.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk da Gwamna da mutanensa sun ki zuwa inda Atiku ya yi taro, duka Sanatocin Benuwai, Suswam, Orker Jev da Abba Moro sun halarci gangamin.
Rahoton ya ce ‘Dan takaran Gwamna a jam’iyyar PDP a 2023, Titus Uba da John Ngbede wanda shi ne abokin gaminsa, ba su biyewa su Ortom ba.
Akwai wasu shugabannin jam’iyyar PDP na reshen Benuwai da ba su bari rikicin ya shafe su ba.
Babu rikici a PDP - Ayu
Da yake magana a wajen taron, Iyorchia Ayu ya yi kira ga Gwamna Ortom da ya hada-kai da Atiku domin jam’iyyarsu ta iya ceto Najeriya a zaben bana.
Dr. Ayu ya ce daya daga cikin Gwamnonin da ke bin tafiyar G5, Okezie Ikpeazu ya shaida masa cewa a shirye yake da ya goyi bayan takarar Atiku a PDP.
The Nation ta rahoto shugaban jam’iyyar hamayyar yana cewa babu wata baraka a PDP, ya ce su na kokarin sulhu da wadanda aka samu ‘dan sabani da su.
Tinubu a garin Katsina
An samu labari Femi Gbajabiamila, Lai Mohammed, Hadi Sirika, Sadiya Umar Farooq, Ali Modu Sheriff sun je kamfen da Bola Tinubu ya shirya a jihar Katsina.
Gwamnonin da suke je yakin zaben sun hada da Nasir El-Rufai, Babagana Zulum, Abdullahi Ganduje, Badaru Abubakar, Atiku Bagudu da kuma wasunsu.
Asali: Legit.ng