Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

  • ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu ya nuna tsakanin shi da Muhammadu Buhari sai dai alheri
  • A jawabin da ya yi wajen taron yawon yakin zabe, Bola Tinubu ya ce babu rikicin komai a tsakaninsu
  • ‘Dan siyasar ya ce duk wani wanda yake ganin Buhari zai yi fada da shi, zai kunyata a fagen siyasa

Nasarawa - ‘Dan takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya tanka masu yada jita-jitar rigimarsa da Muhammadu Buhari.

The Cable ta rahoto Asiwaju Bola Tinubu a ranar Asabar yana mai alwashin kunyata makiyan da suke tunanin yana fada da Mai girma shugaban Najeriya.

Mai neman zama shugaban kasar a zaben 2023 yake cewa duk da Muhammadu Buhari tsohon soja ne, yana bin tsarin damukaradiyya da ka’ida a mulki.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Da yake bayani a wajen kamfe da jam’iyyarsa ta APC ta shirya a jihar Nasarawa, Tinubu ya ce kokarin gyara Najeriya ya hada shi da shugaban kasar.

“Masu tunanin akwai baraka a alaka da abokantakarmu za su cigaba da jin kunya, farin cikin da suke yi ba zai je ko ina ba.
Maganarmu ba batun daidaikun mutane ba ce, ana batun daraja da kishi da kokarin gyara kasa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yakin neman zabe
Yakin neman zaben Tinubu Hoto: @OfficialAsiwajuBAT
Asali: Facebook

Buhari ya yi kokari a mulki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fuskanci kalubalen da suke addabar Najeriya kai-tsaye. Ya yi aiki tukuru kuma sosai.
Mun yi imani cewa ba don tsarin mulki ba, da mun ce ka cigaba da mulki, amma ka dage cewa dole sai ka koma garin Daura.
Ka ce akwai abubuwa da-dama da suka rage kuma za ka kyale mutane su cigaba. Shugabanni irinka ba su da yawa sosai.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

- Bola Tinubu

Premium Times rahoto Tinubu yana mai cewa duk da matsalolin da shugaban ya ci karo da su a ofis, ya cigaba da ginawa Najeriya abubuwa na more rayuwa.

APC ta tsaida kamfe

Dazu nan aka ji Kakakin APC a jihar Oyo, Olawale Sadare ya ce Bola Tinubu ba zai shigo garin Ibadan ba, ya ce halin da ake ciki ya jawo aka fasa taron kamfe.

Mai magana da yawun APC a Oyo ya ce za su karbi bakuncin Asiwaju Bola Tinubu nan gaba ganin yadda karancin Naira da man fetur ya yawaita a ko ina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng