Gwamnan CBN Karya Ya Shararawa Shugaba Buhari: Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

Gwamnan CBN Karya Ya Shararawa Shugaba Buhari: Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

  • Daya daga cikin hadiman shugaban yace sun gani karya gwamnan CBN yake yiwa Buhari
  • Saura kwanaki biyar kacal wa'adin da shugaban Buhari ya kara na daina amfani da tsaffin kudi
  • Shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin Najeriya su bashi kwanaki bakwai kacal ya magance matsalar

Abuja - Babban hadimin shugaban kasa kan lamuran jama'a, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa karyar kawai gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya shararawa shugaba Muhammadu Buhari.

Ngelale yace maganar cewa akwai isassun kudi a cikin gari babu kamshin gaskiya ciki,

Ya bayyana hakan ne a hirar da ya gabatar a tashar TVC inda yace mutane su daina ganin laifin shugaba Buhari, bayanan da ya samu yake amfani da su.

buhari emefiele
Gwamnan CBN Karya Ya Shararawa Shugaba Buhari: Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Ya ce mutane bai zai taba yin abu don tsanantawa jama'a da gayya ba.

A cewarsa:

"Abinda muke yi shine tabbatar da cewa shugaban kasa na samun labaran gaskiya kuma labarin da CBN ya bada cewa an baiwa bankuna isassun kudi a fadin tarayya karyar banza ne. Wannan ya bayyana yanzu."
"Shugaban kasa na jama'a ne, labaran karya kawai yake samu daga wajen CBN, shi yasa aka kara wa'adin daga Junairu 31 zuwa 10 ga Febrairu."

Shugaba Buhari Yace 'Yan Najeriya su Bashi Kwana 7 don Magance Matsalar Sabbin Kudi

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF sun yi tawaga ta musamman zuwa wajen shugaba Muhammadu Buhari game da lamarin karancin takardun Naira a fadin tarayya.

Yan Najeriya na wahala kan rashin isassun takardun Naira bayan tilastasu mayar da tsaffin kudadensu bankuna.

Gwamnonin sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari kokensu inda suka bukaci ya soke lamarin daina da amfani da tsaffin takardun Naira gaba daya.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele Yaudarar Buhari Yayi, Ya Raina Masa Wayau: Adams Oshiomole

Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana cewa babu inda aka taba irin wannan a fadin duniya; inda za'a ce cikin yan kwanaki a kwashe dukkan tsaffin kudade daga hannun jama'a.

Bayan jin kokensu, shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci su bashi kwanaki bakwai kacal don ya magance wannan matsala.

Yan Najeriya har sun fara kwana a gindin na'urorin ATM kawai su samu cire kudadensu na halaliya da suka kai banki da kansu yan kwanaki kadan da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel