Kotun Koli Ta Tabbatar da Kefas Agbu a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Taraba a PDP

Kotun Koli Ta Tabbatar da Kefas Agbu a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Taraba a PDP

  • Dan takarar gwamnan PDP a jihar Taraba ya sha dakyar yayin da batunsa ya je gaban kotu har sau uku
  • Kotun daukaka kara a baya ta bashi gaskiya, a yanzu ma an kuma, kotun koli ta ce shine dan takarar gwamnan Taraba
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan kafin gudanar da babban zaben 2023 da 'yan Najeriya suka dade suna jira

FCT, Abuja - Kotun koli ta tabbatar da Kanal Kefas Agbu mai ritaya a matsayin dan takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan hukuncin ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara na Yola a jihar Adamawa da ya yi watsi da batun kalubalantar sahihancin takarar Kefas.

An samu rikici a jam'iyyar PDP ta jihar Taraba ne bayan kammala zaben fidda gwamin da ya samar da Kefas a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta Tabbatar Da Emmanuel Bwacha Matsayin Dan Takaran Gwamnan Taraba na APC

Kefas Agbu ne dan takarar gwamnan PDP a Taraba
Kotun Koli Ta Tabbatar da Kefas Agbu a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Taraba a PDP | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wannan ne karo na biyu kotu ta yanke hukuncin ba Kefas gaskiya ga kararrakin da abokan mahayyarsa a kujerar dan takarar gwamna; Hilkiah Buba-Joda da Jerome Nyameh suka shigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce wadanda suka daukaka karar sun saba sashe na 84 da 87(9) na kundin dokar zabe ta hanyar kin yin amfani da tsarin zaben fidda gwani da kuma ka'idojin jam'iyya.

Dukkan kotun (na daukaka kara da koli) sun ce, karar da aka shigar bata tushe balle makama, kasancewar basu nemi sulhu a jam'iyya ba tun farko, The Guardian ta ruwaito.

Kotun kolin ya kuma, kasancewar wadanda suka shigar da karar basu hada da sauran 'yan takara ba a batun, don haka sun rasa damar tausayar kotu.

A zaben da aka na fidda gwani a shekarar da ta gabata a Taraba, Agbu ya ci zaben da kuri'u 443 cikin 517 da aka kada.

Kara karanta wannan

Mazan Fama: Sojoji Sun Kai Samame Sansanin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Kwamishina

Laila Buhari ce 'yar takarar sanatan Kano, a cewar kotu

A wani labarin kuma, kotun koli ta bayyana Laila Buhari a matsayin sahihiyar ‘yar takarar sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2023.

Wannan na zuwa bayan da abokin hamayyarta da kuma jam’iyyar PDP suka maka ta a kotu kan bukatar korarta.

A wannan shekarar, an kai ruwa rana sau da yawa kan batun da ya shafi zaben fidda gwani a jam’iyyun Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel