Sarkin Musulmi da Shugaban CAN Sun ba Mabiyansu Shawara a Kan Wanda Za a Zaba
- Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya yi jawabi a wajen taron IDFP da aka shirya kan zabe
- Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga mutane su zabi wanda suke so, ba tare da yin rigima ba
- Shugaban kungiyar kiristoci na CAN, Archbishop Daniel Okoh ya yi makamancin wannan kiran
Abuja - Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci (NSCIA), Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya yi maganar zaben 2023.
Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Juma’a, ya ce Mai alfarma Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya ba mutane shawara a kan zaben shugabanni.
Sarkin Musulmi da Shugaban kungiyar kiristoci na kasa (CAN), Archbishop Daniel Okoh sun yi kira ga ‘Yan Najeriya su zabi wanda suka natsu da su.
Shugabannin kungiyoyin addinan sun ce jama’a su kada kuri’arsu ga wanda suke ganin ya dace, zuciyarsu ta fi karkata da su a zabukan da za a shirya.
Majalisar IDFP tayi zama saboda 2023
Jagororin Musulunci da na Kiristocin sun yi wannan kira a ranar Alhamis a wajen taron neman zaman lafiya a tsakanin mabanbanta addinan kasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majalisar IDFP ta tattauna a kan abin da ya shafi kabilanci da harkar addini a zaben 2023.
Haruna Zubairu ya wakilci Sultan
Punch ta ce Darektan gudanarwa na majalisar NSCIA, Arch. Haruna Zubairu ya wakilci Mai afarma Sarkin Musulmi da Musulman Najeriya wajen zaman.
Arch. Zubairu yake cewa za a fi amfana idan aka zauna lafiya a Najeriya, saboda haka ayi watsi da batun kabilanci a zabe, a fara yin la’akari da kishin kasa.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga al’umma su tanadi PVC, su kada kuri’arsu cikin zaman lafiya ba tare da sun yi wani abin da zai jawo rigima a filin zabe ba.
Assha: Na Kusa Da Buhari Sun Fi Damuwa Da Batun Sauyin Kudi, Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ke Ransa
Sultan yake cewa su zabi wanda suke ganin shi ya dace, su kauracewa wani gurgun ra’ayi, idan sun kada kuri’a, daga nan sai su bar zabi wajen ubangiji.
CAN ta aika Benebo Fubara-Manuel
Rabaren Benebo Fubara-Manuel shi ne wanda ya wakilci shugaban CAN a taron, ya yi kira ga mabiyansa da su ajiye ra’ayin addini da kabilanci a gefe guda.
Benebo Fubara-Manuel a madadin Daniel Okoh, ya ce dole a guji biyewa son rai wajen kada kuri’a. Shi ma bai ayyana wani 'dan takara ko wata jam'iyya ba.
2023 tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu ne
An samu rahoto cewa Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya cire irinsu Rabiu Kwankwaso da Peter Obi a lissafin zaben shugaban kasa da za ayi.
Gwamnan ya ce iyakarta Obi zai samu 1% ne a Sokoto, 2% a Katsina, sai 5% a Kano. A irin haka kuri'un jihohin kudu kurum ba za su ba shi nasara ba.
Asali: Legit.ng