Ina Tare Da 'Aladu' Ne Lokacin Da Na Soki Tinubu, Fani-Kayode

Ina Tare Da 'Aladu' Ne Lokacin Da Na Soki Tinubu, Fani-Kayode

  • Jigon jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Femi Fani-Kayode ya kare kansa kan rubutun da ya yi na suka Bola Tinubu a baya
  • Tsohon ministan sufurin ya ce yana tare da jam'iyyar 'aladu' yana nufin jam'iyyar PDP kenan a lokacin da ya yi rubutun
  • Amma ya ce a halin yanzu ya riga ya ga haske don haka tunaninsa ya canja kuma abin da ke gabansa shine aiki don nasarar Tinubu

Femi Fani-Kayode, Direkta na Karamar kwamitin watsa labarai na kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya yi martani kan rubutun da ya yi kan Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar yan shekarun baya.

Fani Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama na daya cikin manyan masu sukar Tinubu kafin ya koma jam'iyyar mai mulki shekaru biyu da suka shude.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Fani-Kayode
Ina Tare Da 'Aladu' Ne Lokacin Da Na Soki Tinubu, Fani-Kayode. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama sun zarge shi da baki biyu tare da rashin nagarta musamman a kan harkokin siyasa.

Amma, a yayin da ya ke kare kansa a rubutun da ya fitar a Twitter, Fani Kayode ya rubuta;

"Yada rubutun da na yi kan @OfficialABAT shekaru da suka shude ba zai canja komai ba. A lokacin ina jam'iyyar mutane na aladu amma na ga haske na bar aladen. Na dawo APC tuntuni kuma ina yi wa Asiwaju yaki da kowanne tsoka a jiki na don ya yi nasara. Wadanda abin bai musu dadi ba suna iya fadi su mutu."

Duk da bayanin da ya yi, wasu masu amfani da Twitter sun rika tonarsa, ga wasu daga cikin maganganunsu:

Martanin wasu masu amfani da dandalin sada zumunta

Kara karanta wannan

Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

@Philsike1 ya rubuta:

"Kowanne dan Najeriya ya san abin da ya sa ka ke canja rubutu lokaci zuwa lokaci. Ko mutanen ka na APC sun sani. Domin mutum mafi girma a raye a Afirka, Dr Olusegun Obasanjo, ya fada mana kamar yadda ya sanar da wadanda za su zo a gaba."

@ChibuzoUdolisa ya ce:

"Ka manta ka fada cewa dama kana APC kafin ka tafi PDP sannan yanzu ka dawo. Kuma bayan ganin haske, kuma sai dai mutane masu wani irin matsalar gani ke iya ganin hasken daga wuri guda zuwa wani wurin kamar yadda ka ke ganinsa."

@Phemmyjulius ya rubuta:

"Dan siyasa zai sa ka rika kokwanton abin da ke zuciyarka. A kalla idan wani ya yarda ya yi rubutu sai daya amma hakan ya canja da zarar bai babban aljihu ya bayyana, sai biyayya ya samu."

@BullemJoseph:

"Daya daga cikin mafi kyawun rubutun ka. Tun da na fara bin ka, babu abin da zan ce sai godiya ga Allah. Allah ya maka albarka."

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 zai bawa yan Najeriya mamaki, Kwankwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 zai bawa yan Najeriya mamaki.

Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwa cewa shine zai lashe zaben shugaban kasa a zaben da ke tafe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel