Babu Wani Sabon Abu a Cikinsa: Atiku Ya Magantu Kan Faifan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Saki

Babu Wani Sabon Abu a Cikinsa: Atiku Ya Magantu Kan Faifan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Saki

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya yi ikirarin cewa shine dan Najeriya da aka fi bincika
  • Atiku ya fadi haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi kan zargin da aka yi masa a faifan murya da Michael Achimugu, tsohon hadiminsa ya saki
  • A martaninsa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa faifan muryan bao bayyana wani sabon abu ba a iya saninsa

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi martani ga wani faifan murya da Michael Achimugu, daya daga cikin tsoffin hadimansa ya saki.

Kamar yadda ya zo a cikin faifan muryan, an yi zargin cewa Atiku ya bayyana yadda aka kafa wasu kungiyoyi don karkatar da kudaden jama'a.

Atiku da matarsa
Babu Wani Sabon Abu a Cikinsa: Atiku Ya Magantu Kan Faifan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Saki Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Sai dai kuma, a yayin hirarsa da sashin BBC a ranar Talata, 31 ga watan Janairu, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

"Wannan faifan murya bai bayyana wani sabon abu ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa:

"Abun da kawai na sani, an binciki dukkanin sace-sace ko zargin sata da ake yi mun a kasar nan fiye da kowa kuma babu abun da aka gano a kaina."

A cikin hirar, Atiku ya bayyana cewa shine mutumin da aka fi bincika a Najeriya.

Kalli hirar wanda Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter:

Tsohon hadimin Atiku ya fadi manufarsa na son darewa kujerar shugaban kasa

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa tsohon hadimin Atiku Abubakar, Michael Achimugu ya gargadi yan Najeriya a kan cewa kada su kuskura su zabi dan takarar shugaban kasa na PDP a babban zaben kasar mai zuwa.

Achimugu ya ce Atiku na son ya gaje Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne saboda yana kwadaiyin yaransa su zama attajirai da masu iko tamkar shi ko bayan kasa ya rufe idonsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

Ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasar na so 'ya'yansa 31 su mamaye kasar idan ya samu shiga Asorock kamar yadda suke yi wajen sama wa kansu manyan mukamai a jiharsu ta Adamawa.

Ya ce lallai yan Najeriya za su dandana kudarsu idan har suka bari Atiku ya yi nasara a zabe mai zuwa tare da yarda hannunsa ya kai kan baitul malin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng