Takarar Shugaban Kasa: Ka Janyewa Rabiu Kwankwaso: NNPP Ta yi Kira ga Atiku

Takarar Shugaban Kasa: Ka Janyewa Rabiu Kwankwaso: NNPP Ta yi Kira ga Atiku

  • Jam'iyyar NNPP adawa ta caccaki dan takarar PDP kan kiran da yake yi cewa Kwankwaso ya janye masa
  • Atiku Abubakar ya bayyanawa BBC cewa yana tattaunawa da Kwankwaso kan maganar janye masa
  • NNPP ta karyata wannan magana kuma tace Kwankwaso ne ya cancanci a janye masa

Abuja - Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi kira ga dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya janyewa dan takararsu Rabiu Musa Kwankwaso.

Kakakin jam'iyyar ta NNPP, Rufa'i Alkali ya bayyana hakan ranar Laraba a hira da manema labarai.

Ya karyata jawabin Atiku cewa suna tattaunawa da Kwankwaso kan yadda zai janye masa.

Alkali yace Atiku Abubakar ya ji da rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP saboda kansu a rabe yake, rahoton TheCable.

Atiku
Takarar Shugaban Kasa: Ka Janyewa Rabiu Kwankwaso: NNPP Ta yi Kira ga Atiku Hoto: Atiku/Tinubu
Asali: Twitter

A cewarsa:

"Muna ta samun kiraye-kirayen daga fadin kasa. Bamu da wata alaka da Atiku Abubakar ko kadan."

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya

"Rabiu Kwankwaso ne mutum daya da ya nuna cewa ya cancanci zama shugaba a wannan zaben. Atiku ya daina kaskantar da kansa ta hanyar tilastawa yan Najeriya zabensa."
"Shi wanene za'a zaba a Arewacin Najeriya da ya wuce Kwankwasi - tun da maganar arewa ake yanzu? Abinda muke so shine Atiku Abubakar ya janyewa Rabiu Musa Kwankwaso."

Zaben 2023: Yan Najeriya Za Su Mamaki Bayan Ganin Sakamakon Zabe, In Ji Kwankwaso

A wani labarin kuwa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yan Najeriya za su yi mamakin yadda sakamakon zaben shugaban kasan bana zai kasance.

Kwankwaso na cikin manyan yan takara hudu da ake ganin cewa cikinsu mutum daya zai lashe zaben.

Sauran sune dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar; da dan takarar jam'iyyar Labour Party LP, Peter Gregory Obi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Gana Da Atiku Sun Tattauna? NNPP Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Kwankwaso ya bayyana cewa shi ne kadai cikin wadannan yan takara da ya fahimci matsalolin yan Najeriya.

Kwankwaso tare da mataimakinsa, Rabaran Idahosa, sun yiwa yan Najeriya alkawura daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel