APC Ta Yi Wa PDP Wankin Babban Bargo Kan Harin Da Ake Zargin An Kaiwa Buhari a Kano

APC Ta Yi Wa PDP Wankin Babban Bargo Kan Harin Da Ake Zargin An Kaiwa Buhari a Kano

  • Jam'iyyar APC ta karyata ikirarin cewa wasu matasa sun farmaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kano, inda ta bukaci yan Najeriya da su yi watsi da labarin karyan
  • A cikin wata sanarwa daga Bayo Onanuga, daraktan labaran kwamitin yakin neman zaben APC, jam'iyyar ta bayyana rahoton a matsayin wata shiryayyiyar diramar PDP
  • Onanuga ya ce PDP ta daina ganin gaskiya don haka ta koma ga yada karya da labaran kanzon kurege don a dama da ita a siyasa

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana ikirarin cewa wasu fusatattun matasa sun jefi shugaban kasa Muhammadu Buhari da duwatsu a Kano a matsayin hasashen jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), rahoton The Cable.

A wata sanarwa da aka aikewa jaridar Legit.ng, Bayo Onanuga, daraktan labaran kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya ce PDP na ta yi wa shugaba Buhari bita da kulli tun da ta rasa tudun dafawa.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Kamfen din APC
APC Ta Yi Wa PDP Wankin Babban Bargo Kan Harin Da Ake Zargin An Kaiwa Buhari a Kano Hoto: Thisday
Asali: UGC

APC ta magantu kan harin da aka kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari a Kano

A cewar sanarwar, yakin neman zaben shugaban kasa na PDP na durkushewa kuma jam'iyyar bata da wani abu da za ta ja hankalin yan Najeriya don su zabe ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar ta kuma bukaci yan Najeriya da su yi watsi da rahoton domin dai labarin karya da ya fito PDP wacce ke fama da bakin cikin karya tsarin karba-karba.

Onanuga ya kara da cewar PDP na ta daukar nauyin labaran karya a kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, da kokarin haddasa rikici a cikin jam'iyyar mai mulki.

Kakakin na APC ya kuma yio kira ga hukumomin tsaro musannan DSS da ta gaggauta kama kakakin PDP don yi masa tambayoyi kan lamarin rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Laifin APC Da Ganduje Ne Harin Da Aka Kaiwa Buhari a Kano, PDP Ta Tona Asiri

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"PDP jam'iyya ce ta nutse tana rarrafe a kan karya da kuma neman bi ta kowani hali don ganin ta tsaya a saman kogi - amma sai ta nutse a ruwa."

APC ta kara da cewar PDP wacce ta kasance babbar mai sukar shugaba Buhari ta zama mai ci masa albasa a baya-bayan nan saboda shiryayyiyar farfagandanta.

Tinubu ne ya dauki nauyin farmakin da aka kaiwa Buhari a Kano, PDP

A gefe guda, mun ji a baya cewa jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da farmakin da wasu fusatattun mazauna jihar Kano suka kaiwa Buhari yayin da ya kai ziyarar aiki jihar.

PDP ta zargi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da daukar nauyin harin na ranar Litinin 30 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel