Wasu Sun Kona Gidan ‘Dan Takaran APC, Mutane Sun Cafke Wanda Ya Yi 'Aika-Aikar'
- Ezemonye Ezekiel-Amadi ya gamu da ibtila’in gobarar da ta rutsa da wani gidansa a kauyensu
- Mutanen gari sun taimaka sun cafke wani da ake tunani shi ne ya cinnawa gidan ‘dan siyasar wuta
- Ezekiel-Amadi yana neman takarar kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya a jam’iyyar APC
Rivers - Wasu da ake zargin ‘yan dabar siyasa ne sun aukawa gidan Ezemonye Ezekiel-Amadi mai neman takarar majalisar tarayya a zabe.
Punch ta ce bata-gari sun je gidan Ezemonye Ezekiel-Amadi ne da ke garin Omerulu a jihar Ribas, suka cinna masa wuta a karshen makon jiya.
Gidan ‘dan siyasar yana nan a karamar hukumar Ikwerre, yankin tsohon Gwamnan Ribas kuma babban jigo a APC watau Rotimi Amaechi ya fito.
Yanzu haka Ezekiel-Amadi yana rike da tutar jam’iyyar APC mai mulkin kasa yana takarar ‘dan majalisar wakilai na mazabar Ikwerre da Emuoha.
An cafke wani mutum
Rahoton ya ce a lokacin da wutan ta kama ci, matasan kauyen suka yi wuf suka yi ram da wani da ake zargi yana cikin wadanda suka banka wutar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wani bidiyo da Ekekiel-Amadi ya yada, ya nuna cewa gobarar ta cinye mafi yawan dakunansa.
Ana zargin wanda ya shiga gidan ‘dan siyasar domin yin wannan mummunan aiki ya fasa taga ne, sai ya kyastawa labule wuta, hakan ya jawo gobara.
Wani da aka yi nasarar damkewa bayan faruwar abin ya shaida da bakinsa cewa ya fasa tagogin gidan ne, sai ya kyastawa labulayen cikin gidan wuta.
Bidiyon da aka fitar ya nuna an rugurguza duka tagogin gida, sannan kuma kujeru, teburori, silin da kuma kaya da duk wasu na’urorin lantarki sun kone.
Da yake bayanin wannan jarrabawa da ta same shi, ‘dan takaran ya ce dakin wata goggonsa ya kone, ya ce ‘yanuwa da mutanen gari ne suka kawo agaji.
‘Dan takaran ya ce an rasa saman dakin watau silin, na’urar AC, labule da kuma madubin dakin. Jaridar Independent ta fitar da wannan labari a jiya.
Ku na da labari cewa ‘Dan takaran jam'iyyar hamayyar nan ta Hope Democratic Party a zaben 2019 yana kalubalantar kujerar Muhammadu Buhari a kotu.
Cif Ambrose Owuru ya dage sai INEC ta ayyana shi a matsayin asalin wanda ya yi nasara a zaben da ya wuce, A yau kotu tayi fatali da karar da ya shigar.
Asali: Legit.ng